AN NADA ABDULWAHAB SHA’ARANI, SARAUTAR BARAYAN DANBATTA

Daga Muhammad Sakafa, Kanomsakafa@gmail.com

Ranar Asabar 13 ga watan Mayu 2023, ne Sarkin Fulanin Danbatta dake yankin masarautar Bichi Alh. Aminu Bello, ya yi nadin mukaman masarautu kusan guda 40 a yankin Danbatta da kewaye, Wanda aka baiwa ‘yan asalin garin na Danbatta mazauna ciki da wajen garin. Cikin wadanda suka sami wannan babban tagomashin na nadin sarauta har da Alh. Abdulwahab Sha’arani Adamu, babban Dan kasuwa kuma mazaunin garin Kaduna.

An gabatar da nadin sarautun ne a kofar Fadar sarkin fulanin Danbatta, inda ‘yan uwa da abokan arziki da sauran manyan attajirai, ‘yan siyasa dama masu mukaman sarauta suka halarci bikin.

A zantawar da yayi da manema labarai, bayan nadin nasa a matsayin Barayan Danbattan, Alh. Abdulwahab Sha’arani ya nuna farin cikinsa tare da godiya ga Allah bisa wannan tagomashi da ya samu na nada shi wannan matsayi, “ina godewa Allah tare da nuna farin cikina sosai bisa wannan matsayi na nadin saurautar Barayan Danbatta dana samu, sannan ina mika godiya ga sarkin Fulani daya dubeni ya zaboni bisa wannan matsayi da ya nada ni, wannan kuwa ya samu ne sakamakon Sanya albarka ta iyaye da kuma yadda muke zaune da jama’a lafiya”.

Haka nan shima mahaifinsa Alh. Adamu, ya bayyanawa manema labarai irin farin cikin da yake ciki yau na ganin an nada dansa wannan sarauta ” lallai wannan yaro nawa ya cancanci irin wannan matsayi domin yaro ne mai nutsuwa da biyayya garemu iyaye dama duk na gaba da shi, don haka wannan ba abin mamaki bane ga Wanda ya sanshi”. Cikin wadanda suka halarci bikin nadin sarautar sun hada da Dan majalisa mai wakiltar Danbatta da makoda injiniya Hamisu chidari, Alh. Abba tsamiya Danbatta, farfesa Umar Garba Danbatta sai Alh. Ibrahim Amasaye, manyan abokan basaraken Daga kaduna da Abuja da sauran kusoshin gwamnatin tarayya, jiha da kananan hukumomi. Andai yi taron lafiya an tashi lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *