Daga Ibrahim Muhammad Kano

Zababben mataimakin Gwamnan jihar Kano.Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranci kaddamar da fitilu masu aiki da hasken rana da jigo a jam’iyyar NNPP.Alhaji Yusuf Darma ya samar dan sawa a mazabu 13 na karamar hukuma Birnin Kano.

Taron ya gudana ne a yammacin ranar Juma’a a mazabar Zango ya sami halartar masu ruwa da tsaki na NNPP Kwankwasiyya a matakin jiha da karamar hukumar.

Mataimakin Gwamnan jihar Kano mai jiran gado Aminu Abdussalam ya yabawa al’ummar Birnin Kano, bisa gagarumar goyon baya da suka bayar wajen tabbatar da nasarar NNPP. Ya bayyana Alhaji Yusuf Darma wanda shine ya shirya taron na murna da cewa dan jam’yya ne,dan zallar kwankwasiyya da ya bada gudummuwa ta kaiwa ga nasara.

Sannan ya godewa Allah bisa share musu hawaye da ya yi na basu nasara ya yaye musu bakin ciki da masifar Gwamnatin da suka kayar.

Cikin ikon Allah an shiga lungu da sako matasa maza da mata an yi gwagwarmaya.Malamai na soro da makarantun islamiyya da na zawiyyoyi sun yi addu’oi Allah ya tabbatar da nasara.

Kwamred Aminu Abdussalam ya godewa Alhaji Yusuf da yan mazabar Darma da suka shirya taron na murna da jaddada godiya ga Allah bisa nasara da ya yi musu tareda fatan Allah ya fidda su kunyar al’umma Kano gaba xaya.

A jawabinsa wanda ya shirya taron Alhaji Yusuf Darma ya ce sun shiga lungu da sako na karamar hukumar Birni da sauran sassa na jihar Kano sun yi tallan jam’iyya da fadakar da al’umma akan su zabi NNPP.Sun amsa sun zabi Injiniya Abba Kabir da Kwamared shine ma ya shirya wannan taron domin godiya bisa hadin-kai da goyon baya da aka basu.

Darma ya ce ya samar da fitilu masu aiki da hasken rana guda 20 da aka rabawa mazavu domin kyautata tsaro a yankin birnin Kano za’a sa dan hana bata gari fakewa su yi abinda bai kamata ba.

 

A yayin taron kungiyoyi da dama da suka hada da na matasan Daneji sun karrama.Alhaji Yusuf Darma da shaida bisa gudummuwa da ya ke bayarwa.A jawabansu shugaban NNPP na karamar hukumar Birnin Kano da na mazabar zango sun yabawa Yusuf Darma bisa irin gudummuwa da yake bayarwa a tsarin kwankwasiyya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *