Daga Ibrahim Muhammad Kano

Hukumar hana sha da yaki da miyagun kwayoyi (NDLEAl ta kama wasu mutane 85 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a wani gidan rawa da ke Kano ranar Litinin.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kano, kwamandan hukumar na jihar Kano Idris Ahmad Abubakar ya ce kamen ya biyo bayan korafe-korafe kan ayyukan da suka shafi muggan kwayoyi da masu gudanar gidajen rawar suka kai musu ta mayar da wurin na shan miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun hada da maza 55 da mata 30 sannan kuma an kwato wasu abubuwa da ake zargin tabar wiwi c daga hannunsu.

Idris-Ahmad ya kuma ce wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yi yunkurin tserewa.ta hanyar tsallake Katanga yayin da wasu suka yi kokarin buya amma duk an kama wadanda ake zargin.
wanda hakan babbar nasara ce ga hukumar NDLEA a yakin da take yi da ayyukan da suka shafi miyagun kwayoyi a jihar Kano.

Ya ce “Shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi na da mummunan sakamako a cikin al’umma,” in ji shi.

Ya ce wadanda ake zargin suna amsa da tambayoyi ne domin tantance masu sayar da magunguna a cikinsu kafin a gurfanar da su a gaban kuliya.

“Za a tura masu amfani da kwayoyi zuwa sashin da ya dace don ba da shawara,” in ji shi.

Idris-Ahmad ya yi kira ga jama’a da su kai rahoton ayyukan da suka shafi muggan kwayoyi ga hukumar a duk inda suka samu maboyar su a jihar Kano
Pic.
Wasu daga cikin wadanda aka kama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *