Daga Ibrahim Muhammad Kano

Sakamakon watsi da kotu ta yi da karar da wasu shigar akan zaben kungiyar yan kasuwar Galadima.A yammacin ranar juma’a kwamishinan kasuwanci na jihar Kano Barista Ibrahim Muktar ya jagoranci rantsar da sabbin shugabannin da aka zaba.

Tun bayan gudanar da zaben, watanni hudu da suka gabata da Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya yi nasarar sake lashe zaben a karo na biyu da gagarumar rinjaye,amma saboda kalubalantar da wasu yan kasuwar suka yiwa zaben a kotu ba’a rantsar da kunshin zababbun shugabanin ba, har sai da kotu ta tabbatar da sahihancin zaben.

Da yake jawabi bayan rantsuwar,kwamishinan kasuwanci na jihar Kano.Barista Ibrahim Muktar ya ja hankalin yan kasuwar akan su hada kai dan cigaban kasuwar su rungumi kowa ba tare da nuna bambamci ba.

Ya nusar da shugabannin akan cewa su dauka da wanda ya zabe su da wanda bai zabe su ba,da wanda ya kai su kara da wanda bai kai su ba, duk suna karkashin shugabancin sune, suna da hakki daidai da na wanda ya zabe su.

Ya yabawa yan kasuwar ta Galadima da cewa sune mafi zaman lafiya a kasuwannin da suke Kano,dan haka su daure su cigaba da rike kambun, susa dattawa a gaba su girmama su, a karbi shawarwarinsu
Sannan wanda aka sabawa aje a ba shi hakuri a hadu a gyara, a shigo da kowa in an tashi yin kwamitoci na kasuwar a saka su dan a nade sabani gaba daya, sai Allah ya sa albarka a cikin shugabancin.

Da yake zantawa da yan jarida bayan rantsar dasu shugaban kungiyar yan kasuwar na Galadima.Alhaji Mustapha ya godewa yan kasuwar bisa goyon baya da suka bashi na zabar sa a karo na daya suka sake a karo na Biyu, hakan ya nuna irin amincewa da gamsuwa da sukayi da kyautatawa da akayi musu.

Ya yi nuni da cewa zasu tafi tareda kowa,an yi zabe an gama kasuwar Galadima da cigabanta ita ce a gabansu, kowa a kasuwar hakkinsa na wuyansu a matsayinsu na shugabanni, babu wani da za su ware su ce shi bai yi su ba a zabe,za su cigaba da yiwa kowa abinda ya dace dan jin dadin yan kasuwar.

Alhaji Mustapha Shu’aibu ya ce za su yi iya yanda za suyi su kawo cigaba su zauna da gwamnati lafiya dan a sami cigaba da bunkasar yan kasuwar da yan kasuwar .

 

 

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *