Daga Mansur Aliyu

Jaridar LEADERSHIP Hausa ta rasa shugaban sashen fassara, Malam Sabo Ahmed Kafin-Maiyaki wanda ya rasu a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu, 2023 yana da shekaru 54 a duniya bayan doguwar jinya.

A cewar sanarwar da iyalansa suka fitar, Malam Sabon, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 10 da kuma dan uwa guda daya.

Jaridar IDON MIKIYA ONLINE NEWS,  ta sami  cewa, za a yi jana’izarsa a yau Juma’a, 19 ga watan Mayu, 2023 a layin Mangwarori Hayin Dogo Samaru, Zaria, da karfe Goma na safen nan a Jihar Kaduna.

Da yake tabbatar mana da rasuwa, daya daga Editocin jaridar LEADERSHIP HAUSA wato Malam Bello Hamza, cikin dare, ya bayyana mana cewa tabbass Malam Sabo Ahmad, ya rasu.

Sabo kuma shi ne mai kula da shafin laifin kotu da dan sanda na Leadership Hausa.

Da fatan Allah ya gafarta mashi ya kuma sanya aljannah ta zamo makomarsa.

Bugu da kari shugaban kanfanin na Jaridar IDON MIKIYA ONLINE NEWS, Alhaji Mansur Aliyu ya kuma jajanta wa iyalan mamacin da dukkan abokan aiki sa na  kanfanin Jaridar Leadership, da daukacin yan jaridu baki daya, inda ya bayyana alhininsa game da rasuwar ma’aikacin da suke tare da dadewa, cikin aminci

“Allah ya bai wa iyalansa juriyar wannan rashi da suka yi.”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *