Daga Bello Hamza, Abuja

A halin yanzu kungiyar ‘Grassroot Mobilizers for Better Nigeria Initiative’ wadda Ambasada Dakta Fatima Muhammad Goni ke shugabanta, ta bayyana goyon bayanta da cancantar Hon. Abbas Tajuddeen a gwagwarmayar shugabancin Majalisar Wakilai ta 10 da ake yi.

Dakta Fatima Goni ta bayyana haka ne a tattaunawarta da manema labarai a Abuja, ta kara da cewa, kungiyar su nada wakilci a matakin karkara a fadin Nijeriya musamman ganin suna kuma taimaka wa al’umma ba tare da nuna bambanci ba.

Ta ce, sun amince da akidar rarraba mukamai ga dukkan bangarorin kasa don kowa ya san ana damawa da shi. “Duk da fitowarta daga jihar Borno ina goyon bayan a bai wa bangaren yankin Arewa maso gabas shugabancin Majalisar Wakilai, a kuma nemi kwararre wanda  ya san gobe, ya san mutuncin mutane kamar Hon. Abass Tajuddeen, don kwararre ne kuma mutumin kirki ne an riga an masa yabo kyakkyawan yabo da zai tafi da gidan domin ya yi sau daya sau biyu sau uku har sau hudu, an kuma ga yadda ya gudanar da harkokinshi” in ji ta.

Ta kuma bayyana cewa, a karkashin kungiyarsu ta Grass Roots, akwai tsangayoyi akwai marayu da sauran su duka an dukufa ana addu’ar Allah ya bashi nasara na Speaker kuma InshaAllah shi ne Speaker mu na 10 assembly da yarda Allah da amincewarta sa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *