Daga. Ibrahim Muhammad Kano

Gwamnatin jihar kano ta miƙa muhimman bayanan gwamnatin ga kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP dake karkashin jagorancin Shugaban kwamitin Dr Abdullahi Baffa Bichi.

Sakataren gwamnatin jihar kano Alhaji Usman Alhaji shugaban kwamitin miƙa mulki na jam’iyyar APC ya mika muhimman bayanan a madadin gwamnatin mai barin gado a gidan gwamnatin kano.

Ya yi godiya ga kwamitin karɓar mulki bisa basu hadin kai har suka samu nasarar kammala aikin da aka dora masu, tareda godewa sakatariyar su bisa yadda suka yi aiki ba dare ba rana dan ganin an kammala aikin.

ya ce sun Sami fahimta juna sosai wajen gudanar da aiki saboda dukkanin bangarorin magana suke ta yadda za’a ciyar da jihar kano Gaba.

Shugaban kwamitin karɓar mulki na jam’iyyar NNPP Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya yabawa kwamitin miƙa mulkin Saboda yadda suka gudanar da aikin tattara bayanan.

Ya ce za su je su duba muhimman bayanai da suka karba sannan su bada shawarwari ga sabon gwamnan kano Engr. Abba Kabir Yusuf domin duba yadda za’a inganta rayuwar al’ummar jihar kano..

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *