An Gudanar Da Taron Jin Ra’ayoyin Al’umman Sabon Gari, Akan Tattara Tashoshin Mota Waje Guda

*Daga Nasiru Adamu*

Karamar hukumar Sabon Garin Zariya, ta yi taron jin ra’ayoyin al’umar dake cikinta, domin bada shawarwari game da kudurin da karamar hukumar ta dauka na tattara dukkanin tashoshin mota zuwa sabuwar tashan Samaru da ta Yankarfe.

Taron wanda aka gudanar da shi a babban dakin taron ofishin hukumar gudanar da aikin Hajji dake Dogarawa, ya sami halartan shuwagabanin al’umma tare da wakilan jami’an tsaro daban daban dake cikin Karamar Hukumar.

Jim kadan bayan kammala taron, shugaban taro Hon Ishaqa Idris, wanda kuma shine Kansilan mazabar Bomo, ya yi wa manema labarai karin haske dangane da manufar taron, yayin da ya ce sun kirayi al’ummane domin jin ra’ayin su tare da bada nasu gudunmowar shawarwari akan komawar tashoshin guri guda. Da kuma yadda za a cimma nasaran yin hakan.

Sannan ya bukaci al’umman da su kara hakuri da wannan sabon tsarin da aka samu a halin yanzu kafin a saba, kuma insha Allah, za a sami nitijan hakan nan bada dadewaba musamman wajen rage cinkoso da samun ingantacen tsaro a dukkanin fadin Karamar Hukuma.

Haka nan shima kakakin majalisar Karamar Hukumar Sabon Gari, Hon. Aminu Yusuf, ya bukaci dukkanin al’ummar dake cikin Karamar Hukumar, da su kasance masu karban wannan tashoshin hannu bibbiyu domin rage bata gari da suke samun mafaka a tashoshin da ake da su barkatai a halin yanzu.

Daga bisani ya jinjinawa Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari Hon. Engr. Muhammad Usman, dangane da jajurcewarsa wajen ganin al’umar Sabon Gari, ta sami ingantatu ayyukan ci gaba.
Sannan ya yi godiya ga dukkanin al’ummar Karamar Hukumar Sbon Gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *