Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bude masallacin juma’a da ya kunshi filin Idi,dakin wankin gawa na Inuwa Dutse tareda kaddamar da cibiyar addinin musulunci ta Muhammad Inuwa da ya kunshi makarantar Islamiyya da Asibiti da dakin karatu.

Da yake jawabi wazirin Kano.Alhaji Sa’ad wanda ya wakilci sarkin Kano.Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya al’ummar yankin murna bisa samar musu da cibiyar da masallaci.

Ya yi kira ga al’ummar akan raya masallacin da kuma godewa iyalai da zuriyar marigayi Inuwa Dutse bisa assasa wannan aiki na alkhairi da suka dauka.

Shima a nasa jawabin Alhaji Aminu Alhasan Dantata ya ce babbar rana ce a wajensa zuwa bude wannan masallaci da cibiyar da aka kafa.
Ya ce sun saba da marigayi Inuwa Dutse tun basu hadu a gwamnati ba suna aminci har sukayi aiki suka rabu a cikin gwamnati suna tare da girmama juna da kauna.Iyalansa sun dauke shi uba shima ya dauke su ya’ya.

Alhaji Aminu Dantata ya ce Malam Inuwa Dutse mutunin kirki ne.Sannan ya yi kira ga al’umma ayi ta addu’a a halinda aka sami kai a kasar nan Allah ya daidaita al’amurammu a koma kan daidai.
Ya yi fatan wannan cibiya da masallaci da aka assasa.Allah ya dada karfafa shi ya bunkasa sosai ya kuma basu ikon taimakawa a ciki.

Da yake gabatar da jawabi a madadin ya’yan marigayin.Dokta Abdullahi Inuwa Dutse ya ce sunyi niyyar samar da wani abin alkhairi ne mai dorewa da zai amfanar da al’umma wannan tasa suka sa niyyar yin wani aiki da niyyar wanzuwar ladan ga mahaifinsu da Allah ya yiwa rasuwa ranar 6 ga rabi’ul akhir 1439 daidai da 4/12/2017.Shekaru Biyar da wata biyar da suka wuce.

Ya ce wannan ya sa su iyalansa suka hada kai dan bada wannan gudummuwa ga al’ummar Sallari,Karkasara,Sheka,Hausawa,Gyadi-gyadi,Darmanawa da sauran unguwanni makota.

Dokta Abdullahi ya ce sun godewa Allah wannan cibiya da masallaci sun zama kyakkyawan misali na sadaka mai gudana Allah ya gafartawa malam ya saka mass da alkhairi.

Ya ce sun cimma nasarori a kokarin kafa wannan cibiyar da suka hada da kammala ginin masallaci da ta zama cibiya ta hada kan al’ummar musulmi da bauta da neman kusanci ga Allah.Suna data cibiyar ta kasance dalilinta ta kara musu kusanci ga Allah da neman yardarsa.

Abdullahi ya ce cibiyar ta kunshi masallaci da shirin gina makarantar Islamiyya,karamin Asibiti da sairan abubuwa da zasu taimaki al’umma.

Ya ce masallacin na Inuwa Dutse da Alhaji Aminu Dantata ya bude gini ne mai hawa Biyu da za’a rika salla ta kullum da ta juma’a da sallar Idi.Wajen sallar maza a kasa da ofishin liman,akwai wajen sallar mata da dakin bincike da karatu.Akwai rufin masallacin da ya kunshi karin wajen sallar akwai ban dakunan maza 15 na Mata Bakwai da dakin yiwa gawa wanka da ofishin yan agaji da rijiyoyin burtsatse dan amfanar al’umma.

Suna shirye-shirye dan ganin sun kammala wadannan ayyuka a gajeren lokaci da zasu ba su damar bada gudummuwa wajen inganta ilimi da kyautata zamantakewa a tsakanin al’umma.

Dokta Abdullahi Inuwa Dutse ya bayyana cewa akwai aminci da kauna tsakanin Aminu Dantata da mahaifinsu rasuwar sa ba ta sa ya dauke hannunsa daga ya’yan sa ba da kuma bada gudummuwa wajen aikin gina cibiyar.

Shima Ambasada Usman Inuwa Dutse yace shine da kusan na 20 a cikin ya’yan marigayi Inuwa Dutse da suka kai 35 yace mutane sun yiwa mahaifinsu shaida na alkhairi ya zauna da mutane lafiya shi yasa Allah ya dubi bayansa suka hadu sukayi masa sadakatul jariya.

Ya ce Malam Inuwa Dutse mutumne mai tausayi da son addini da tallafawa marayu da suma suke dan kwatantawa.

Usman Inuwa Dutse ya yi wa ya’yansa tarbiyya ta dogaro da kai ya basu ilimi kuma masu sha’awar kasuwanci ya tallafa musu da suma suke koyi da amfani da tarbiyya da ya yi musu.
Sarkin Dutse Alhaji Hamim.Nuhu Muhammad Sunusi na daga cikin wadanda suka halarci bude masallacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *