Daga Ibrahim Muhammad Kano

Zababben Dan majalisar tarayya mai wakiltar Birnin Kano Injiniya Sagir Ibrahim Koki ya ce a kokarib kawo cigaba a jihar Kano yan majalisun tarayya na jihar Kano gaba daya sun hada kai domin yin magana da yawu guda dan kyakkyawan wakilci da zai amfani jihar Kano.
Ya bayyana hakanne da yake zantawa da yan jarida a ya yin taron ya ye matasa maza da mata guda 174 da aka koyawa sana’ar dinki da sauran sana’oi karkashin “kwankwasiyya tailoring empowerment association”
Ya ce abin ban sha’awa gaba daya.yan majalisar Kano sun hada Kansu waje guda duk masu neman shugabaci na majalisa abinda suke. Fara tambayar su shine me suka tanadarwa Kano?Wane abu za su yiwa jihar Kano. Kuma suna basu amsoshi wanda da yardar Allah al’ummar Kano zasu dulmiya cikin romon damakwaradiyya da yardar Allah.
Injiniya Sagir Ibrahim Koki ya ce “Abin sha’awa a matsayina na dan majalisa karkashin jam’iyyar NNPP an nada ni a matsayin ko’odineta na duk yan majalisun tarayya da suke jihar Kano ba NNPP ba APC kowa yana karsahimmu saboda suma sun fahimci cewa akidar mu itace mai kyau su rabe damu a tafi tare azo a yiwa al’umma abinda ya dace”.. cewar Injiniya Sagir.
Ya kuma yabawa kungiyar da ta shirya taron na ya ye dalibai da aka koyawa sana’oi hakan ya karfafa masa gwiwa ganin yanda mutane ke amfani da damar su dan ganin sun koyawa matasa sana’a dan dogaro dakai.
Injiniya Sagir Ibrahim Koki ya ce za suyi amfani da damarsu na hada kan yan majalisu domin tallafawa irin wadannan kungiyoyi da wadanda suke koyawa sana’oi dan amfanar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *