Ibrahim Muhammad Kano

An yi kira ga al’umma kan su yi hakuri da sabuwar gwamnati saboda za’a ga canje-canje da sai anyi hakuri an jure an jajirce domin kowa da irin salon mulkinsa.
Janar manaja na rukunin kamfanonin Gerawa.Alhaji Ibrahim Muhammad ne ya yi kiran da yake zantawa da manema labarai a Kano a ya yin wani daurin aure na ya’yan manajan kamfanin shinkafa na Gerawa a masallacin Zurfan.

Ya yi nuni da cewa ba lallai ne abinda za’a fara da shi wani ya ga ya yi masa dadi ba,amma in akayi hakuri za’a ga nasara kuma za’a ji dadi a gaba da yardar Allah.

Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa ya ce kullum dan’adam baya karbar canji da wuri,amma in an karba anyi hakuri anyi addu’a ba abinda za’a gani a gaba sai alkhairi.

Ya ce su kuma sabbin masu mulki da suka karba ayi musu addu’a ba ruwansu da cewa wannan nawa ne,wannan ba nawa bane. Dukkan wanda yake wannan jihar a karkashin Gwamna ya ke kuma gwamna na da damar hukunci a kan sa.Sannan shima za’a tambaye shi akan hukunci da adalci da ya yiwa kowane mutum.

Alhaji Ibrahim Muhammad Gerawa ya ce babban fatan su a wajen sabbin Gwamnoni da shugaban kasa shini Allah ya taya su riko ya taimakesu su yi adalci ga kowa.

Da yake nasiha ga ma’aurata ya ce Aure muhimmin abune a rayuwa da ake fatan samun iyali nagari da yake bukatar hakuri da fahintar juna da soyayayya a tsakanin mata da miji.

Shi ma Muhammad Isyaku daya daga iyaye, yace abin jin dadi ne da godiya ga Allah ne ya nuna maka ranarda zaka aurar da ya’yan ka cikin rayuwar ka.

Alhaji Muhammad Isyaku wanda shine Manajan Darakta na kamfanin shinkafa na Gerawa ya godewa Al’umma da sukazo dan taya su murna ya yi fatan Allah ya zaunar da kasar nan lafiya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *