Gwamnatin jihar Zamfara ta yi fatali da wani labari da aka yaɗa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa Gwamnan Jihar Dauda Lawal ya bayyana kadarorinsa na kimanin Naira Tiriliyan Tara.

A cikin wata takardar sanarwa ga manema labarai, mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a yau Juma’a a Gusau, ta bayyana labarin a matsayin ƙage da ƙarya da aka tsara domin karkatar da hankalin sabuwar gwamnati daga tafarkin ceton jihar Zamfara. Sannan ta ce wannan ci gaban ƙarairayin waɗanda suka faɗi zaɓe ne, kamar yadda suka yi ta yi a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ya ƙara da cewa sabuwar gwamnati ta fara aiki kuma ta mayar da hankali ne wajen ganin ta kawo tunani mai kyau da ake da buƙata a harkokin gudanar da mulki a jihar domin gudanar da ayyukanta.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “An ja hankalinmu kan wani mummunan labari da aka yaɗa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana kadarorin da ya kai kimanin Naira Tiriliyan Tara. Gwamnati ta takura ne ta fitar da wannan sanarwar domin ance ƙaryar da ake ta maimaitawa (kuma ba a ƙalubalance ta ba) a kan iya kallonta a matsayin gaskiya.

“Wannan shifcin gizon da ƙaryar da aka ƙirƙira kuma aka yaɗa ta a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne maɓarnata ne ke yi da niyyar karkatar da hankalin sabuwar gwamnati.

“Sharuɗɗan da suka shafi bayyana kadarori suna cikin dokokin ɗa’a na jami’an gwamnati, wanda ke ƙunshe a cikin sashe na 1 na jadawali na biyar na kundin tsarin mulki na 1999, kamar yadda aka yi kwaskwarima cewa dole ne dukkanin ma’aikatan gwamnati su bi, kuma ya kasance sirri ne a ma’adanar hukumar ɗa’ar ma’aikata.”

“Dukkan jami’an gwamnati tun daga shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, Gwamnoni, da duk zaɓaɓɓun jami’ai da ma’aikatan gwamnati dole ne su cika su kuma gabatar da wannan fom ɗin bayyana kadarorin kamar yadda doka ta tanada. Dauda Lawal ya bi ƙa’idojin kundin tsarin mulki kuma abubuwan da ke cikin su sirri ne ga hukumar, wacce ta kasance hukuma mai mutunci da ƙwarewa.”

“Ba za a ɗauke mana hankali daga waɗannan labaran ƙarya na kafafen sada zumunta ba, domin gwamnatinmu tana da alƙibla kuma ta maida hankali wajen magance matsalar tsaro, ilimi, ruwan sha, kiwon lafiya, noma da sauran ƙalubalen zamantakewa da tattalin arziƙi da suka addabi jihar. Muna kuma aiki ba dare ba rana domin ganin mun sauke nauyin da ya rataya a wuyanmu wanda Gwamna ya rantse a kai.”

“Mun ɗora ɗamban aiki kuma muna da ayyuka birjik da za mu yi a ƙoƙarinmu na ceto da sake gina jihar Zamfara mai inganci tare da kuma ci gaba da mai da hankali wajen ganin mun cika alƙawuranmu. Muna kira ga al’umma da su yi watsi da wannan ƙaryar da ake yaɗawa da gangar domin a karkatarwa tare da ɓata sunan wannan sabuwar gwamnati a jihar Zamfara.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *