Daga Ibrahim Muhammad Kano

An rantsar da sabbin shugabanin Kungiyar canjin kudi na Al,amanat na Wapa a safiyar Litinin din nan bayan gudanar da zabe da akayi a makonnin baya.

Da yake jawabi bayan shan ratsuwa sabon zababben shugaban kungiyarAlhaji Sani Salusu Dada da akafi sani da Mati igo ya yi kira ga yan kasuwar su taimaka musu dan yin shugabanci nagari.

Ya ce kofarsa a bude take domin karbar shawara da zata amfanar dasu wajen gina cigaban kasuwar Wapa.

Dada ya yi nuni da cewa kungiyar na da matsalar samun kudin shiga na gudanarda ayyukanta kuma ba wata kungiya da zata tafi sai da kudin shiga, dan haka akwai bukatar ya’yanta su bada goyon baya na sama mata kudaden shiga.

Dan haka nema a sakamakon daukewa yan kasuwar karbar kudin haraji na watanni Uku,shi a kashin kansa ya baiwa kungiyar kyautar kudi N1,000,000 tareda kira ga yan kasuwar suma su taimaka da gudummuwa da kungiyar zata tafi da harkokinsu.

Sabon shugaban na Al’amanat Alhaji Sani Dada ya yi kira ga jami’an tsaro da cewa Idan wata sabuwar doka ta fito ta da ya shafi sana’arsu su rika sanar da kungiyar dan su sanarwa mambobinsu sannan idan matsala ta taso akan dan kungiyar a sanar da shugabanni dan daukar mataki.

Dada ya jaddada cewa shugabancin kungiyar da aka zabe su a shugabanci ba da wasa za suyi ba,za su yi da gaske ne, dan kawo gyara da zai amfani kasuwar ta Wapa, sannan suna fata Allah ya basu ikon tafi da kungiyar cikin nasara.

Shima jami’in hulda da jama’a na kungiyar .Abdullahi A Wapa ya shaidawa yan jarida cewa ya yi an rantsar da sabbin yan kungiyar karkashin Alhaji Sani Salusu Dada da mataimakinsa Alhaji Mustapha Muhammed Rago da sakatare Alhaji Haruna Musa Halo da shi a matsayin mai magana da yawun kungiyar da sauran shugabanni.

Abdullahi A Wapa ya ce tunda aka kirkiri Wapa samada shekaru 50 ba’a taba fitowa anyi zabe na damakwaradiyya kamar na wannan karon ba na zabar cancanta da zata mai da Wapa sabuwa fil da yardar Allah kamar yanda aka zabi Abba Kabir Gwamna a Kano da suke masa datan zai taimaki cigaban Kano kamar yanda sabon shugaban Wapa Sani Dada zai taimaki mambobi ya yi aiki ya gyara kasuwar ya tsaftace ta saboda yanada kudurori da manufofi na alkhairi da inganta tsaro.

A lokacin taron rantsuwar yan kasuwar da dama sun bada gudummuwar kudi da aka tara makudan kudade da zai tallafawa cigaba da gudanarda harkokin tafi da kungiyar.Taron ya sami halartar wakilan shugabannin jami’an tsaro da kungiyoyin kasuwanni na Kano.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *