Daga Ibrahim Muhammad Kano
Gwamnan jihar Kano, Injiniya . Abba Kabir Yusuf ya nemi goyon baya da hadin kan bangaren majalisar dokoki ga bangaren zartarwa domin a samu kyakyawar alakar aiki tsakanin su domin ci gaban jihar kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi sabbin shugabanni da ‘yan majalisar dokokin jihar Kano da aka zaba a karkashin jam’iyyar NNNP a qarqashin sabon shugaban majalisar Rt. Hon,. Jibril Ismail Falgore wanda ya kai masa ziyara a gidan gwamnati jim kadan bayan an rantsar da majalisar ta goma.
Gwamnan ya taya sabbin shugabanni da sauran ‘yan majalisar murnar qaddamar da sabuwar majalisar tare da addu’ar Allah Ta’ala ya yi musu jagora wajen sauke nauyin da ke kansu na yin doka da kuma alaqa da sauran vangarorin gwamnati cikin kwanciyar hankali da lumana.
Hakan dai na cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai.
Ya tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na yin aiki a matsayin turaku biyu wajen tafiyar da mulki da kuma cigaban jihar kano mai albarka
A nasa jawabin sabon shugaban Majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore ya ce sun ziyarci gwamnan ne domin gabatar masa da sabbin shugabanni da mambobin sabuwar majalisar tare da jaddada aniyar yin aiki da bangaren zartaswa domin cimma burin da ake bukata.
.