Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad Duguri, ya aike wa Majalisar dokokin jihar sunayen mutum ashirin da uku (23) da ya zaba a matsayin Kwamishinoninsa da yake bukatar Majalisar za ta tantance tare da amincewa da su a matsayin Kwamishinoni kuma mambobin Majalisar zartaswar jihar.

A yayin zaman Majalisar na ranar Litinin da kakakin Majalisar, Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman ya jagoranta ne, Majalisar ta samu sakon gwamnan Bala Muhammad da ke neman a amince da zabin da ya yi wa mutanen a matsayin Kwamishinoni.

Shugaban masu rinkaye na Majalisar, Saleh Hodi Jibir ne ya karanta sakon na gwamnan.

Kamar yadda yake a jerin sunayen da gwamnan ya aike, karamar hukumar Alkaleri ta samu zababbun Kwamishinoni biyu Maiwada Bello (Geo Barrister) da Ibrahim Gambo; kazalika ita ma karamar hukumar Bauchi ta samu zababbun Kwamishinoni biyu wato Mahmoud Babamaji Abubakar da Hon. Danlami Ahmed Kawule, Sai kuma saura kananan hukumomin sun hada da Bogoro: Tsammani Lydia Haruna; Dambam: Ahmed Sarki Jalam; Darazo: Yakubu Ibrahim Hamza; Dass: Usman Santuraki; Ganjuwa: Abdul Hassan; Gamawa: Muhammad Salees; Giade: Dr. Yakubu Adamu.

Saura su ne: Jama’are: Usman Abdulkadir Moddibo; Itas/Gadau: Hajara Jibrin Gidado; Katagum: Hon. Farouk Mustapha; Kirfi: Hajara Yakubu Wanka; Misau: Aminu Hammayo; Ningi: Hassan El-Yakub, SAN; Shira: Muhammad Hamisu Shira; da kuma Tafawa Balewa: Silas Madugu.

Har-ila-yau a karamar hukumar Tafawa Balewa, gwamnan ya zabo Abubakar Abdulhamid Bununu; sannan, ita ma karamar hukumar Toro ta na da zababbun Kwamishinoni biyu Jamila Muhammad Dahiru da Dr. Adamu Umar Sambo; Warji: Abdulrazak Nuhu Zaki, sai kuma a karamar hukumar Zaki, gwamnan ya zabi Amina Muhammad Katagum a matsayin wacce yake so a matsayin Kwamishinoni.

A cikin sanarwar manema labarai da mai magana da yawun kakakin Majalisar, Abdul Ahmad Burra, Hon. Barr. Habibu Umar (Da ke wakiltar mazabar Kirfi) ya bada shawarar Majalisar ta ware ranakun 2, 3 da 4 na watan Augustan 2023 a matsayin ranakun tantance Kwamishinoni. Sai ya samu marawar bayan Hon. Lawan Dauda (Mazabar Sade).

Daga nan Majalisar ta amince da ware ranakun 2, 3 da 4 domin aikin tantance zababbun Kwamishinonin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *