Daga Mansur Aliyu Zaria 

A shirye-shiryen kara habaka harkokin gudanarwar jihar ta Kaduna da kuma cika alkawuran yakin neman zabensa, mai girma gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da nade-naden mukamai kamar haka:

Mohammed Sada Jalal – Babban Darakta mai kula da hukumar kula da gine-ginen jihar Kaduna (KADGIS).

Jerry Adams – Mukaddashin Shugaban Hukumar Tattara haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS). Adams zai yi aiki a matsayin shugaban zartarwa har zuwa lokacin da za a nada babban shugaban zartarwa.

Adamu Magaji – Babban darakta na Hukumar Kula da kayayyakin Gwamnatin Jihar Kaduna (KADFAMA).

Adamu Sama’ila – Mai bada shawara na musamman kan harkokin ma’aikata.

Amina Sani Bello – Babbar mataimakiya ta musamman kan al’amuran Dalibai.

Salisu Ibrahim Garba – Babban Mataimaki na Musamman kan harkokin Siyasa.

Larai Sylvia Ishaku – Babbar Mataimakiya ta Musamman kan harkokin zamantakewa da cigaban jama’a.

Clement Shekagoza Wasah – Babban Mataimaki na Musamman kan harkokin Al’umma.

Waziri Garba – Babban Mataimaki na Musamman kan harkokin Gudanar da gwamnati.

Nade-naden an yi shine bisa duba da cancanta da jajircewarsu wajen yi wa jihar Kaduna hidima da kuma tabbatar da ajandar ci gaba ta sabuwar gwamnati.

Daga karshe Gwamnan ya yi musu fatan Alkhairi tare da jan kunnensu wajen sauke nauyin da ke kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *