Daga Ibrahim Muhammad Kano
An gudanar da taro karo na Bakwai akan ranar tunawa da cikar jam’iyyar NEPU shekaru 73 da kafuwa taron da cibiyar nazarin damakwaraxiyya ta jami’ar Bayero ta gudanar a gidan Mumbayya a ranar Talata.
Da yake gabatar da jawabi a yayin taron furofesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana cewa siyasar akida ce ke biyan bukatun jama’a, duk da jam’iyyar NEPU bata kafa Gwamnati ba,amma ta tsaya ta jajirce wanda yanzu ne ake ganin nasarar da ta cimma.
Ya ce dagewar da NEPU tayi ta kwatowa talaka yancinsa yanzu, misali a tsarin kananan hukumomi an dabbaka shi a kasa,duk da ba ita take gudanar da mulki ba.Amma gwagwarmaya da tayi ta kwatawa dan talaka yanci, yanzu fiye da kashi 70 ko 90 na masu mulki ya’yan talaka ne.
Ya kara da cewa ba dan irin wannan gwagwarmayar ba, ya’yan talaka ba za su sami damar har su shiga a dama dasu kamar yanda ake yanzu ba.
Furofesa Kamilu Sani Fagge ya yi nuni da yanda a yanzu kuma al’amura suke tabarbarewa fiye da na da yanda akayi gwagwarmaya a baya aga an canza lamarin.Dan yanzu ma yakamata ayi.Mutane su kada su ja hannunsu su zauna,fitowa za suyi su dage su ga cewa sun zabi shugabanni amintattu an kafa Gwamnati mai adalci da zata biya bukatun al’umma.
Furofesa Kamilu Sani ya ce yin irin wannan fafutuka sai an dauke kwadayi da kin yarda ayi amfani da kudi a juya ra’ayin mutane, sannan kuma sai mutane sun kashe kasala kar su gajiya wajen zaben shugabanni nagari.In anaso a kawo canji dama na hannun jama’a ne, domin. talakawa sune keda yanci da iko su iya canza irin wannan al’amari, basu nade hannu kawai suna jira abubuwa su canza dan kansu ba, dole sai an jajirce ta yin abinda yakamata kamar yanda yan NEPU suka yi.
Shima mai masaukin bakin taron Daraktan Cibiyar nazarin Damakwaradiyya na jami’ar Bayero na gidan mumbayya.Furofesa Habu Muhammad Fagge da yake zantawa da yan jarida ya ce yanzu an sami kai a kasa irin ta Najeriya mai arziki, amma talauci ya dabaibaye mutane, wadanda suka kada kuri’a su sun yine da zimmar cewa, za’a ceto su daga kanginda suke ciki, amma aka sami akasi talauci dada katutu yake ma.
Ya ce yanzu abubuwan rayuwa na habaka yana kuma gujewa talaka yana shiga matsi, amma kuma su masu madafan mulki abubuwan rayuwa ke dada bunkasa a garesu, hakan ya tabbatar da cewa siyasa ta akida irin ta NEPU da akayi yanzu babu irin ta, sai dai ayi kokarin yanda za’a ja hankalin mutane su karkata wajen yanda za’a gyara a daidaita bakin zaren.
Habu Muhammad Fagge ya yi nuni da cewa yanda za’a gyara bakin zaren ana bukatar su kansu jam’iyyu ya kasance ba’a yaudari masu zabe ba,su kuma masu zabe basu yaudari kansu ba.Mu zabi mutum nagari na kowa, da aka riga aka san akida da yake da ita kadai zata iya canza alkibla na talaka.
Ya ce su kuma jam’iyyu ya kasance sun dauki abinda ake bukatar aga sunayi, shi ne fadakarwa, domin yawa-yawan jam’iyyu basa fadakarwa, domin in suka fadakar ta yaya za’ayi su yaudari jama’a. Rashin yin hakan sai gashi an sami kungiyoyin sa kai ne suke fadakarwar, wanda jam’iyyu ne yakamata suyi, sannan idan jam’iyya zata fadakar,fadakarwar ta gyara ce.Amma jam’iyyun da yawansu ba hakan suke ba, sai dai kurum akai mutane cikin duhu, azo kayi zabe yau a ranar da aka rantsar da mutum,sai ya fadi wani abu da daidai yake da ya kashe rayuwar talaka.
Furofesa Habu Fagge ya kara da cewa suma yan jarida hakkin sune su fadakar domin mutane su fahimta cewa akida da tsari irin na jam’iyyu aiwatar dashi yanda yakamata shine abinda yakamata ayi a wannan lokaci domin a kawo canji.
Ya bada misali da cewa kasashe da suka cigaba a damakwaradiyya su,idan kace za kayi a,b da c idan ka sami Gwamnati bakayi a,b,c ba ka tafi kana z,d da f, to ka shiga a uku babu ma wanda zai dada zabenka,amma anan a yayinda kazo kayi siyasa ta kudi,za’a zo a zabe ka.”Da mu da jam’iyyu ana bukatar canji sai anyi karatun ta natsu dan a kawo gyara ga kasa in ana bukatar damakwaradiyya ta doru a kan doro na gyara na canji.
Furofesa Habu Muhammad Fagge ya ce akwai yakinin kasar nan na da arziki da dukkan makotanta ba su da irinsa ,amma babban abinda yake faruwa jagoranci ya yi mana wuya wala’alla baragurbin shugabanni muke zaba,to yakamata wajen fitar da shugabanni mu tsaya mu zabi mutane ba yan jari hujja ba, wadanda zasu kaimu ga tashar naki wadanda zasu kaimu ga cigaba da zasu canza rayuwarmu ta inganta ba tareda kabilanci ko banbanci na launi ko bangaranci ba, kasar za’a sa a gaba ayi abu saboda Allah a aiwatar da abinda aka fada, ba yaudara ba,wadannan abubuwa matakai ne in akayi amfani da su kuma mu yi ikirarin cewa, duk jam’iyyar da bata aiwatar da duk abinda tasa a gaba na allheri ba, a dawo ayi waiwaye in an zo zabe kar a zabi dan takarar da ta tsayar.