Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana mataimakin shugaban majalisar Dattajai ta kasa Rt. Hon. Sanata Barau jibrin da cewa mutumne da yake daukar nauyin al’umma birni da kauye ba’a iya ka shiyyar sa kawai ba harma jihar Kano da kasar nan baki daya.Alhaji Lawan Abdulhamid Sheka daya ne daga tsofaffin daraktocin Sanata Barau jibrin a karamar hukumar Kumbotso shine ya bayyana hakan da yake zantawa da yan jarida a Kano.

Ya ce tun daga fara siyasar Barau zuwa yanzu da duk irin al’ummar da yake tare dasu kowa ya san mutumne mai karamci da ya san darajar dan’adam da martabarsa da mutunci mutum bai yarda ya wulakanta wani ba haka ba zai yarda na kasa dashi ko wadanda suke kusa dashi su wulakanta wani ba.

Ya ce shi shaida ne a tsawon shekaru da suke tare da shi,sai dai duk lokacinda akace al’umma sun taru da yawa za’a sami bambamcin fahimta na kowane irin mutane.A baya shekaru 20 Barau yana Kano ba shida mukamin komai bayan ya yi dan majalisar tarayya na Tarauni yana gida yana harkokinsa zai je al’amura na jama’a daurin aure,ta,aziyya da sha’ani daban-daban na mutane wanda ya fi saukin ganuwa a lokacin.

Ya ce cikin ikon Allah ya zo ya zama kwamishina a wata Gwamnatin baya nan kullum yana tare da jama’a.Lokacinda ya zama sanata Barau ya kan bar Abuja kusan duk mako ya zo ya gana da mutanenda zuwa Abuja tayi musu nisa ba zasu iya zuwa ba,kuma can wuri ne na aikin al’ummar Nijeriya ba kawai Kano ko shiyyar sa ba.

Ya yi nuni da cewa yanzu kuma likkafa taci gaba idan jama’a zasu kalla da kyau wadanda ke bada tsaro ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa Barau I jibrin ayau ba wadanda suke a baya bane saboda yanzu ya zama wata kadara ta Najeriya gaba daya bata jihar Kano Kadai ba saboda haka dukkan jami’an tsaronsa hankalinsu na kansa domin tsare lafiyarsa da kwanciyar hankalinsa saboda haka dole za’a sami bambanci da yanda aka zauna a baya da kuma yanzu.

Alhaji Lawan ya ce maganar wasu makusantan Barau I Jibrin na hana mutane kaiwa gareshi ba gaskiya bane,wannan magana babu ita ba dalilinta Baurau din da aka sani na jiya shine yau shine kuma gobe a abubuwanda ya keyi na alkhairi na girmama dan’adam da darajar tashi.

Da ya juwa kan maganar daurin aure da akayi na dan majalisar Dattawan na Kano ta Arewa da diyar dan majalisar wakilai na karamar hukumar Dala duk da cewa sun bambanta a jam’iyya yace ita siyasa akwai take da ake mata na siyasa bada gaba ba,sannan siyasa mu’amala ce ba abune na yaki ko gaba ba.

Ya ce shi yasa yake kaicon shugabanni da in suna bayani suke maganar kiyayya a siyasa wacce ita kuma ba maganar kiyayya sai sai hamayya yau in baka tare da mutunci gobe zaku iya haduwa a wata jam’iiyya.

Ya ce daurin auren ya nuna darasi babba da yakamata al’umma su gane manyan nan shugabanni ne na al’umma duk Wanda ya sami dama al’ummar sa yake kokari ya hidimtawa ya kyaitatawa to na kasa da suna koyi da yanda manya ke mu’amala da a kasa ba za’a sami fitintinu ba.
Ya yi nuni da cewa in kana rigima akan wane wancan na yi akan wani ga irinta watakila sai ya’yanku su so su hada Ku zumunci da ba zai kare ba,za’a hayayyafa ayi ya’ya da jikoki na kasa yaje can yana rigima ko yana jin haushin wani akan wani hakan ba daidai bane.

Alhaji Lawan Abdulhamid Sheka ya ja hankalin magoya bayan yan siyasa na kasa masu tasowa yanzu suke harkar siyasa su sani siyasa mu’amala ce dan kana jam’iyya A,wani na B a sani duk Wanda duk ya sami magana ce ta yaya za’a hidimtawa al’umma yanda za’a kyautata musu ba maganace ta rigima ko ta gaba ko fada ba.Dan haka mutane suyi koyi da irin wannnan abin da ya faru.Sanata Barau na jam’iyyar APC shi kuma dan majalisar tarayya na Dala Ali Madaki yana NNPP jam’iyyar adawa, amma wannan bata hana anzo an hada auratayya ba a tsakanin ya’ya dan haka a gane zama lafiya da fahimta da addu’a Allah ya bada shugabanni nagari ne mafi muhimmanci ba gabar siyasa ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *