A ranar Laraba da daddare ne ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Gidan-damo da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara inda suka kashe mutane uku tare da raunata bakwai tare da sace wasu takwas.

Wani mutumin yankin mai suna Umar Sani ya shaidawa wakilin IDON mikiya online news cewa ‘yan bindigar da ke kan babura sun isa kauyen ne bayan sallar isha’i , inda nan take suka bude wuta kan wadanda suka ci karo da su.

Sani ya ce, mutane uku ne suka mutu nan take sannan wasu bakwai sun samu munanan raunuka.

Ya kuma bayyana cewa, sauran mutanen kauyen sun gudu zuwa daji domin tsira da rayukansu.

A cewarsa, daga baya ‘yan fashin sun koma gida gida inda suka yi garkuwa da wasu mata hudu tare da ‘ya’yansu hudu sannan suka koma dajin.

Ya ce, “Mun kammala sallar Magrib bayan karfe bakwai na daren Larabar da ta gabata, sai muka ji karar harbe-harbe da dama”.

“Kafin mu fahimci abin da ke faruwa, sai kawai muka ga wasu gungun ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suna harbe-harbe kai-tsaye.”

“Sun harbe mutane uku har lahira a nan take tare da jikkata wasu bakwai”.

“Sun kuma bi gida-gida suka sace mata hudu tare da jariransu hudu suka koma dajin”.

Sani ya ci gaba da cewa, jami’an tsaron da aka sanar da abin da ke faruwa sun isa kauyen bayan ‘yan bindigar sun bar yankin.

Duk kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Yazid Abubakar ya ci tura domin bai amsa kiran waya ba bayan an yi yunkurin yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *