Daga Abubakar M Taheer

Haske Children Foundation ta gudanar da gwaje-gwaje gami da bada magani kyauta ga yara Masu Bukata ta Musamman a Kaduna.

Gidauniyar wanda ta ƙunshi kwararrun likitoci da ungozama sun gudanar da wannan aikin ne sakamakon halin kunci da al’umma suke a ciki.

Dr. Fatima Zangina kwararriyar likita ce ta bayyana wa manema labarai makasudin wannan taron.

“Munzo nan ne domin bada magani, gami da gudanar da gwaje-gwaje da bada kyautar abinci ga yara Masu Bukata ta musamman dake fama da jinyoyi daban-daban”.

Yawanci yaran suna fama da jinyoyi da ake kallo a matsayin abun ƙyama a cikin al’umma wanda kuma hakan kan saka yaran shiga halin damuwa.

Malama A’isha Muhd daga Unguwar Malali, ta bayyana dalilin zuwan ta wannan taron,

“Na kawo yarana 3 wanda suke fama da jinyoyi daban-daban wanda hakan kan saka mu damuwa nida mai gidana, amma Alhamdulillah likitoci sun bamu magani sun kuma nuna masa jinyoyi su ana iya warkewa gaba daya”.

Itama a nata Zantawa da Manema Labarai Shugabar Gidauniya ta Haske Children Foundation, Fatima Bello ta bayyana cewa ya zuwa yanzu suna da fatan ace yara sama da dari biyar ne suka amfana da wannan kyautar maganin da bada abinci kyauta gasu masu bukata ta musamman.

Fatima Bello ta bayyana farin cikinta kan yadda al’umma musamman iyaye mata suka amsa gayyata tare da kawo yaransu. “Muna gode musu da amanar da suka bamu Allah ya Bama yaransu lafiya”.

Wani Yaro Mai bukata ta musamman ya bayyana min cewa ya sami ganin likita tare da bashi magani kyauta gami da abinci. Inda ya nuna yana cikin farin cikin.

A wani bincike da aka gudanar a shekarar 2011, Nijeriya tana da masu bukata ta musamman miliyan 25 wanda a cikinsu miliyan 3.6 suna fama da cutukan masu haɗari ga rayuwarsu musamman yara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *