ZAMFARA : An Gudanar Da Addu’a Na Musamman Kan Matsalar Tsaro
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Sakamakon mawuyacin halin da jama’ar Jihar zamfara ke ciki biyo bayan hare-haren ‘yan bindiga, wasu kungiyoyi sun gayyaci al’ummar musulmi a fadin jihar domin gudanar da addu’oi na musamman.
Taron ya gudana ne a yau Alhamis a filin Edi da ke Tudun Wada Gusau. Taron dai ya sami halartar malamai da makarantun Islamiyya da kungiyoyin addini da daliban makarantun firamare da sakandare na jihar.
Daga cikin abin da ya gudana a yayin taron sun hada da karatun Alkur’ani mai tsarki da addu’o’in zababbun malamai karkashin jagorancin Dokta Atiku Balarabe Zawiyya Gusau, tare kuma da wa’azi da dai sauransu.
Da yake nasa jawabi, kwamishinan ma’aikatar ilimi da kimiyya da fasaha, Malan Wadatau Madawaki, ya ce dangane da ma’aikatarsu, a shirye suke su bada dalibansu domin halartar irin wannan taro don Gudanar da addu’o’i a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Kwamishinan wanda ya wakilci Babban Sakatariyar ma’aikatar, Dr. Barira Ibrahim Bagobiri, ya kara da cewa, sace daliban da aka yi a makarantunsu ya tilasta musu barin daliban su shiga wannan addu’oi, sai dai ya yi kira ga jami’an tsaro da su rubanya kokarin da suke yi na dakile duk wani bala’in da ke faruwa a jihar Zamfara da ma kasa baki daya.
Shima da yake nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya taron addu’o’i na musamman Farfesa Nasiru Anka, ya ce sun yanke shawarar shirya addu’o’i na musamman a filin Sallar Idi na Gusau, bisa la’akari da dimbin al’ummar Musulmi da za su halarci addu’o in.
Ya ce, jihar Zamfara na da kalubalen tsaro, kuma hanyar da za a bi wajen dakile matsalar ita ce a koma ga mahalicci, a nemi taimakonsa, domin a cewarsa komai daga Allah yake, kuma dole ne kowane mai imani ya san haka.
A karshe ya sanar da cewa, za a rika gudanar da irin wannan zaman addu’a lokaci zuwa lokaci, har sai mun shaida karshen wannan aika-aika na ‘yan fashi da makami a wannan Jihar tamu, in ji shi