Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau 

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana shirin yin hadin gwiwa da kasar Sweden a bangarori daban-daban da suka hada da hakar ma’adinai da Noma da makamashi da Kuma harkar ilimi da kiwon lafiya a fadin jihar Zamfara.

Gwamna Dauda Lawal ya karbi bakuncin jakadiyar kasar Sweden a Najeriya, Annika Hahn-Englund a makon jiya a ofishinsa da ke Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa ziyarar jakadan kasar Sweden ta ba wa bangarorin biyu damar tattaunawa a tsakaninsu.

A cewar sanarwar, Gwamna Lawal ya kuduri aniyar binciko duk hanyoyin da za a bi don jawo hannun jarin kasashen waje da tallafi daga abokan huldar kasa da kasa.

“Taron na da nufin samar da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki masu muhimmanci da kulla alaka mai dorewa, da aiwatar da ayyukan da za su kawo sauyi domin amfanin jihar al’ummar jihar.

“A taron, Gwamna Lawal ya tabbatar wa Jakadan kasar Sweden a shirye gwamnatinsa ta ke don inganta hadin gwiwa da ci gaba mai dorewa a bangarori daban-daban.

Bugu da kari, jakadan ya yi alkawarin baiwa jihar kwararun fasaha a fannin hako ma’adanai da dabarun noma na zamani da samar da makamashi da tallafawa wajen inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *