Daga Ibrahim Muhammad Kano.

Hukumar zsbe mai zaman kanta ta kasa ta yiwa mutane samada mutane Miliyan 93 rijista domin kada kuri”a a zabe da yake gabatowa.
Shugaban Hukumar na kasa furofesa Mahmud Yakub ne ya bayyana haka da yake ganawa da jam’iyyu 18 da suka tsaida yan takara.
Yace daga cikin wadanda sukayi rijistar katin zaben samada mutane Miliyan 40 mata ne,Miliyan 49 maza,sannan daga adadin fiyeda mutum Miliyan 37 matasa ne da suke wakiltar kashi 39 cikin 100 na rijistar
Mahmud Yakub ya tabbatarda cewa INEC ta cimma nasarar muhimman abubuwa guda 11 daga cikin tsare-tsarenta 14 na shirye-shiryenta na tunkarar zabe mai zuwa.
Yace yanzu hukumar na tsaka da gudanarwa a yanzu shine na Rana katin zabe na dindindin ga masu rijista.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *