An Nada Sabon Sarkin Magina A Masarautar Hayin Dogo Dake Gundumar BOMO Zariya

Daga Nasiru Adamu

Ranar juma’ar makon da ya gabatane Sarkin Hayin dogo Alhaji Shehu Musa, ya jagoranci nadin Bikin sarautu uku a kofar Gidansa dake Hayin do go Samaru Zariya.

Daga cikin mukaman Sarautar da aka nada sun hada da Sarautar mai Unguwa da Sarautar Sa’i da Sarautar Sarkin Magina wanda aka baiwa Malam Abdullahi Isiya.

Jim kadan bayan kammala bikin nadin Sarautar da aka gabatar, Wakilinmu ya tuntubi Sarkin Maginan Malam Abdullahi Isiya dangane da wannan  karamcin da aka yi masa, na

Sai ya tabbatar mana da cewar zai yi kokarin kawo ci gaba wajen hada kan Maginan yankin, su kasance tsintsiya madauriki daya, ta yadda zasu kafa gungiya mai rijista da hukuma.

Sa’annan kuma a gefe guda kuma zai tabbatar da an sami ci gaba wajen fahimtar juna tsakanin Magina da sauran Al’ummar gari musamman masu bada filayensu domin ginawa.

Haka nan ya dauki alwashin daidaita farashin gini  domin samun matsakaicin farashin tsakanin mai gini da Al’umma.

Daga bisani ya yi addu’ar fatan alkairi ga Sarkin Zazzau Ambasada Nuhu Bammali, tare da hakimin Gundumar Basawa Alhaji Mannir Jafaru, da yan Majalisarsa, game da gudumuwar da suke badawa wajen samar da zaman lafiya a lardin Zazzau baki daya.

Daga karshe ya Jinjinawa Sarkin Hayin Dogo Alhaji Shehu Musa, a bisa karamcin da ya yi masa wajen bashi wannan Sarautar, kuma ya yi masa fatan gamawa lafiya a bisa jagorancin da yake gudanar wa yankin Masarautar Hayin Dogo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *