Abinci Da Ake Nomawa A Arewa Ya Isa Ya Ciyar Da Ƙasar nan. In Ji Farfesa Sabo Muhammad

Daga Abubakar M Taheer

Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammad ya bayyana irin damarmakin da Arewacin kasar ke dashi wajen noma dama ciyar da al’umma ƙasar.

Haka kuma kasar tana da hanyoyin kasuwancin kayan abincin tsakanin ƙasashen duniya.

Farfesa Abdulkarim ya bayyana haka ne a taro karon Farko da Masana kimiyyar Abinci Suka gabatar a Jami’ar Bayero dake Kano.

Taken taron na bane de shine” Samar wa Abincin da ake nomawa a Arewacin Kasarnan gurin Zama a Kasuwanni Duniya”.

Farfesa Abdulkarim Ya bayyana cewa Nijeriya na daya daga cikin kasashen da ake alfahari da ita a Afrika dama duniya baki daya da Allah ya horewa kasar noma.

Farfesan ya bayyana irin yadda masana daga ko’ina a faɗin duniya suke gabatar da ƙasidun albarka noma da kasar take dashi kama daga noma Masara,Dawa, Gero, Maiwa dss.

“Wanda da ace shugabannin kasar nan zasu haɗa hannu da masana, cikin kankanin lokaci kasar zata zama abun kwatance a duniya dama samun hanyoyin shigowar kudi ga ƙasar.

Ana ta Jawabin Shugaban Kungiyar Masana Kimiyyar Abinci ta Arewacin Maso Yamma, Dr. Zahra’u N Bamalli, ta bayyana cewa manufar wannan taron shine shigo da masana kimiyyar Abinci daga ko’ina a faɗin Arewacin Kasarnan domin haɓaka yankin gaba.

Dr. Zahra’u N Bamalli ta kara da cewa, tun asalin Arewacin Nijeriya nada tarin abinci wanda ake yi su tun iyaye da kakanni, wanda ya zama dole ga masana su rinka yin nazari dama fito da amfanin su domin ingantawa gami da gogayya da sauran taƙwarorinsu na duniya.

” Ya zame mana dole mu rinka inganta abinci gargajiya tare da shigo da dabarun alkinta yadda ake yinsu, domin kula da lafiya al’ummar dama kare su daga barazanar kamuwa da cutuka wanda aka iya kamuwa ta hanyar rashin inganci abinci.

Idan ya zama an inganta abinci mu, aka shigo da dabaru zamani wajen yinsu, nan gaba kadan Arewacin kasar zai zama abin kwatance.

Dr Zahra’u N Bamalli ta kara da cewa, muna so irin wannan taron ya zama wata inuwa da zata rinka hada, Masu bincike, Masana, Shuwagabannin, dama Masu kamfanonin sarrafa abinci dake arewacin kasar nan.

Tunda farko ƙwararrun masana, daga Sassa daban daban-daban sun gabatar da ƙasidu, Haka kuma taron ya samu halartar Ɗalibai daga Masu daga cikin jami’o’i Kasarnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *