Daga Ibrahim Muhammad Kano

An samarda cibiyar koyar da harshen turanci na “AL-ASAD English Academy”ne domin horar da dalibai da sauran jama’a samun kwarewa a kan harshen ganin yanda ake samun rauni sanin turancin ga yan makaranta.
Daraktan cibiyar Isah Mu’azu Alhasan ne ya bayyana hakan da yake zantawa da yan jarida ya ce an kafa shekaru sama da 12 suka gabata don kawar da i matsalar da al’ummar Hausa ke samu a turanci.

Ya ce a makarantu na furamare da sakandire da manyan makarantu yaran hausawa basa iya fahimtar darasussuka in basu da turanci dan haka suka kirkiri nakarantar Dan taimakawa al’umma su koyi turanci dan fahimtar darusssa yanda ya dace a duk matakin karatun da za su yi.
Isah Ma’azu Alhasan ya ce shiya kafa makarantar kafin sauran mutane su zo su bashi goyon baya manufar da tasa ya kafa makarantar shima ya fada irin yanayin.

Ya ce ya soma da aji guda daya da dalibai guda Bakwai shine malami da yake koya musu jin dadin karatun da karbuwa ya kara bunkasa makarantar wanda a yanzu sunada dalibai kusan 200 da malamai Bakwai.

Ya kara da cewa dalibai.da suka ci gajiyar makarantar tun daga kafata za su kai 3000.Wadanda aka ya ye kuma aka baiwa shaida sun kai 34 akwai wadanda su dama ba shaidar karatu suke nema ba suna karatunne su kware su tafi.

Ya ce dalibansu sun kunshi wadanda basu taba makaranta ba da wadanda suka karatun a matakai daban-daban ko digiri da digirgir kayi idan Kana da rauni na fahimtar turanci zaka iya karatu a cibiyar.

Ya ce kalubalensu shine na rashin wadatar samun kudaden shiga na gudanarwa yanda yakamata duk da suna samun dauki da gudummuwa na shawarwari da taimako daga masu makarantu irin nasu.Irinsu M.M Haruna da Kabiru Musa jammaje da Jamilu Ciroma.

Malam Isah Ma’azu Alhasan ya ce tsarin karatun nasu shine sau biyu a nako kuma na tsawon awanni biyu a rana daidai da yanayin lokacin dalibi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *