Daga Idris Umar Kaduna

Mai girma Alhaji Awwal Musa Ijakoro wani bawan Allah ne a cikin al’ummar kasar Bwari dake Abuja

Cikin hikimar Allah sai Allah ya woshi zai zama jagora ga Al’ummarsa

Koda yake ya fitone daga gidan sarauta tun assali wasu ma tuni suke girmashi  a matsayin shugaba wanda yeke da tausayin jama’a gashi jinin sarauta ne a jikinsa amma kuma a karkashin wannan baiwar Allah yayiwa mai martaba kwarjini da ilmin sanin yadda ake zama lafiya da Al’umma kamar yadda ya taso yaga mahaifinsa nayi.

An haifi mai martaba Alhaji Awwal Musa Ijakoro ne a garin Bwari ta birnin tarayya Abuja a ranar 9 ga watan yuli 1977.

Cikin ikon Allah a yanzu Alhaji Awwal Musa Ijakolo shine Sarkin Bwari mai daraja na biyu.

Wannan mukami Allah ya dorashine a ranar 24 ga watan oktoba shekarar 2017 kuma har zuwa yau shike karagar mulki.

Alhaji Awwal na samun yabo sosai ga jama’arsa manya da yara.

Mai martaba Alhaji Awwal Musa Ijakoro ya gaji wannan sarautace gurin mahaifisa Alhaji Musa Muhammad Ijakoro wanda a hannunsa masarautar ta zama mai daraja ta biyu a 12 ga Satan Yuni 1997 wanda ya rike har zuwa 29 ga watan agustan 2017 wanda daga bisani shi mai martaba Alhaji Awwal Musa ya gajeshi mahaifin nasa a halin yanzu.

Bincike ya nuna daukakar da masarautar tasu ya biyo bayan umurnin da marigayi shugaban kasa Janar Sani Abacha ya baiwa ministan Abuja na lokacin Janarar JT Usaini, daya kara daukaka jarajar masarautun dake birnin tarayya Abuja.

Wanda kasar Alhaji Musa Muhammad Ijakolo na daga cikin masaratu 14 da suka sami daukaka a lokacin kuma a shekar 2017.

A shekarun da mai martaba Alhaji Awwal Musa Ijakoro yayi akan kujerar mulki ya sami nasarar hada kan al’umarsa waje guda wanda hakan ya kawo mashi daukaka a masarautarsa baki daya.

Batun ilmi kuma mai Martaban yayi karatun primary ne a suleja a shekarar 1984 zuwa 1989 a makarantar da ake kira Aliyu wali ta jihar Niger.

Mai martaba yayi karatun secondary a makarantar GSS kwali Abuja a 1997.

Daga 2001 zuwa 2003 mai martaba yayi karatun dufuloma akan harkokin Gwamnati a jami’ar Abuja wanda daga nanne ya fara rike mukamin gargajiya.

Ya yi aikin a gwamnati musamman a makarantar Shari’a ta Nijeriya reshen Bwari daga 2000 zuwa 2010.

Bisa hazaka da mai Martaban yake dashi ne al’umna ke mashi fatan alheri tare da addu’ar kariya gareshi a kodayaushe

Yayin hada wannan labarin ne muka sami labarin  rasuwar mahaifiyarsa wanda muke masa jaje da tausayawa tare da nemawa mamaciyar gafara ga Allah.

shi kuma Allah ya bashi hakuri.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *