Daga Ibrahim Muhammad Kano

Zababben Gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar NNPP.Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya gayyaci al’ummar jihar Kano zuwa Hukumar Zabe reshen jihar Kano,dan shaida miƙa masa shaidar lashe zaben Gwamnan Kano tare da mataimakinsa, Kwamred Abdulsalam Gwarzo da za’a gudanar gobe laraba.

Sanarwar hakan na kunshe ne cikin sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ga manema labarai a ranar Talata.

Sanusi Bature ya ce gangamin karbar shaidar zai gudana ne Sakatariyar hukumar zaɓe da ke Kano ya yi fatan mahalarta taron zasu kiyaye bin dokok

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *