Daga Ibrahim Muhammad Kano

Ambasada  Sani Muhammad Hotoro daratan walwala na yakin neman zabe na jihar Kano na takarar Injiniya Abba Kabir Yusuf kuma daya da yan kwamitin karbar mulki ya yi kira ga al’ummar Kano su baiwa sabuwar Gwamnati mai shigowa goyon ba

Yace nasarar jam’iyyar su ta NNPP na zabar injiniya Abba kabir a matsayin Gwamnan kano abune da ita Gwamnati mai barin gado take gani kamar ba zai yiwu  ba, sai  gashi ya yiwu, domin babu abinda ya gagari Allah wanda dashi suka dogara ya kuma  tabbatar musu da nasara, suna godita gareshi  akan haka

Ya ce yanzu ma, za su je suyi aiki da kwamiti da Gwamnati mai barin gado ta jihar Kano zata kafa,za suyi aiki tare na tsare-tsaren karbar mulki wannan alama ce ta nuna yardar su, da cewa NNPP ta ci zabe, kuma zasu bada mulk

Ambasada dan Sani Hotoro yace suna rokon Allah ya yi riko da hannun mai gidansu Injiniya Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya sa su fita  kunyar  al’ummar jihar Kano

Sannan Ambasada Sani Muhammad ya yi wa mutanen jihar Kano albishir da cewa, mai gidansa.Injiniya Abba Kabir Yusuf zai yi aiki tukuru a Kano kamar yanda babansa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi da yardar Allah.Duk mutanen jihar Kano sun yarda Kwankwaso ya yi Gwamnati irin wacce al’ummar da  suke son cigaba suke bukata.Kuma hakika Abba Kabir Yusuf zai yi irin wannan tareda dori bisa shawarci da neman gudummuwar Kwankwaso.

Ambasada Dan Sani ya yi kira ga mutanen Kano gaba daya, akan su baiwa wannan zababbiyar Gwamnati ta Abba Gida-gida hadin kai a ciyarda jihar Kano gaba, yanzu ba magana ake ta siyasa ko ta yan jam’iyya ba.Su a wajen jagoransu ya jaddada musu cewa magana ake ta jihar Kano yanzu, dan haka mutanen jihar Kano su so su bada hadin-kai ayi Gwamnati da kowa zai aminta da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *