Daga Ibrahim Muhammad Kano

Daya daga cikin jigo kuma fitattun matasa a karamar hukumar Gwale, Hon. Abdulhad Dalhatu Awilo ya fice daga cikin jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar PDP har kuma ta bashi damar zama dan takarar majalisar dokokin jihar Kano daga Gwale.

Awilo ya tabbatarwa da manema labarai ficewar tasa inda yace ya fita daga APC ya koma PDP sakamakon rashin adalci da shugabanin jam”iyyar suke a karamar hukumar Gwale.

Ya ce jam’iyyar APC ta koma ta wasu yan tsirarun mutane a Gwale basa kulada muradun  kananan  yan jam’iyya dan yana cigaba da neman takara ta majalisar jaha a karkashin PDP kuma a wajen Allah suke nema tareda neman goyon bayan al’ummar Gwale su mara masa baya domin kaiwa ga gaci.

Hon.Abdulhadi Awilo yayi nuni da cewa tun 2011 da suke a cikin jam’iyyar PDP har suka zo APC suke cigaba da hidimtawa a karamar hukumar Gwale amma ko a kwamitin yan shara ba’a tava kiransa ance ya kawo yaronsa ko shi yazo ayi dashi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *