Daga Bello Hamza

Gamayyar Kungiyar manoma ta Najeriya AFAN, ta Mika sakon taya murna ga mabiya addinin kirita bisa kewayowar ranar bukin kirisimati na wannan shekarar ta kuma mika sakon taya murnar sabuwar shekara ta 2023 ga daukacin Yan Najeriya.

Shugaban Kungiyar ta AFAN Akitetc Kabir Ibrahim cikin wata takardar manema labarai da ya fitar ya bukaci daukacin manoman kasar, wadda Kaso saba’in cikin Dari kananun je da matsakaita, da su kara kaimi wajen ganin sun Wadata kasar da abinci duk kuwa da kalubalen da annobar Corona ta haifar ta fuskar koma baya a gare su cikin shekarar 2020 da 2021 da 2022 da kuma kalubalen tsaro gami da tsadar takin zamani da kuma ambaliyar ruwan sama da yayi sanadiyar tafka hasarar dumbin dukiya ga manoman.

Kazalika, shugaban kungiyar ya bukaci manoman na Najeriya su kasance masu magana da murya daya a koda yaushe su kuma guji Yan barandan da ke ci da gumin manoma domin ganin sun kai ga biyan bukatar duk abunda suka sanya a gaba.

Bugu da Kari, kungiyar ta AFAN tayi fatan ganin an gudanar da babban zaben Najeriya da ke tafe cikin kwanciyar hankali da lumana tare da Kira ga mambobinta da su zabi shuwagabanin da suke da yakinin zasu bunkasa harkar noma a kowani mataki yayin zaben na badi.

A karshe, Akitetc Kabir Ibrahim ya nanata Kira ga manoman Najeriya da su kasance masu bin doka da oda a koda yaushe domin ciyar da kasa gaba.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *