Daga Ibrahim Muhammad Kano

.
A yayind a ranekun da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta tsayar za’a gudanarda zabubbuka a kasarnan al’ummar jihar Kano na yin tururuwa zuwa ofisoshin hukumar na kananan hukumomi domin karbar katin zabensu na dindindin.
Zagayenda wakilin jaridar Idon mikiya/tactual news ya gudanar a kananan hukumomin Birnin Kano,Dala da Nasarawa yaga mutane da dama maza da mata na yin layin karbar rijistar.
Wani matashi da muka samu a ofishin hukumar zaben na karamar hukumar BIrnin cikin cincirindon mutane yana bin layin ya karbi katinsa yace sammako ya yi large Takwas na safe amma da zuwansa sai yaga wasu tuni sun rigashi Dan haka shima ya shiga layi kuma tunda ana karba za’azo Kansa.
Sai dai wasu kuma a ofishin Inec din na Gandun albasa sun koka da cewa aikin bada katin na lakaki sakamakon rashin yawaitar masu dubo katin amma duk da haka ana baiwa mutane.
Haka abin a kananan hukumomin Dala da Nasarawa nan ma jami’an hukumar zaben na iya kokarinsu wajen baiwa mutane katin.
Wani ma’aikacin INEC din a karamar hukumar Nasarawa da yace karnu bayyana sunansa yace abinda yasa ake samun tururuwar jama’a shine saboda gabatiwar zabe da a baya anata kukan mutane basa zuwa amma yanzu saboda wayar da kai da ake yasa mutane ke cincirindo.
Ana ganin matakinda INEC ta dauka na bayar kai katunan zaben mazabu zai sa mutane su karbi katin cikin sauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *