Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugaban kungiyar”AKY brotherhood campaign forum for Abba Kabir Yusuf 2023″ Alhaji Bashir Abubakar yace wannan kyakkyawar nasara da Allah ya maimaita musu kamar yanda suka samu a 2019 aka hanasu, gashi Allah ya maimaita gaskiyar sa, ya tabbatar da Abba Kabir shine Zababben Gwamnan jihar Kano.

Ya ce da yardar Allah al’ummar Kano za suyi farin ciki da jin dadi da annashuwa,domin tun 2019 suke hakkon yanda za’a kawo cigaba a Kano sai wasu mutane marasa daraja suka kawo matsaloli,suka sa Kano a wani yanayi, yanzu Allah ya amsa addu’ar al’umma ya kwato jihar Kano.

Alhaji Bashir Abubakar ya ce a matsayinsu na yan’uwa ga Abba Kabir za su fito kwai da kwarkwata su baiwa zababben Gwamnan shawarwari yanda zai amfanar da harkokin jama’a ya gudanarda mulkinsa cikin adalci.

Alhaji Bashir Abubakar ya yi nuni da cewa a fafutukarsu na ganin Abba ya yi nasara, sun sha kalubale da wahala sosai,musamman su da suke qaramar hukumar Gwale mahaifar Gwamna Abba, wanda suna tareda shugaban jam’iyya ta yan adawa,sun ga abubuwa da yawa na cin zarafi, su da iyayensu da ya’ya sharruka iri-iri ba wanda ba su gani ba.Amma da yake Allah ba azzalumi bane, gashi Allah ya tabbatarwa Abba nasara.

Yace babban burin su, shine yanda Kano za ta ci gaba,duk wani abu ma da akayi musu na vatanci,sun barwa Allah, ba za su waiwayi wani abu na baya dan ramuwa ba.

Shugaban na “AKY Brotherhood campaign 2023” Ya ce su yanzu kowa a Kano nasu ne,kamar yanda Allah ya damkawa Abba wannan kujera ta Gwamna zai yi adalci akan kowa, domin sun san Abba Kabir Mutum ne jajirtacce,me gaskiya da riqon amana،Tun da suka taso dashi a matsayin wa bai tava gani wani yazo masa da tsegumi ya yarda ba.

Ya ce shi abinda Abba ya ke so shine, ka kawo masa shawarar yanda zai taimakawa mutane,wanda zai hada zumunci bama a zumunce ba, jihar Kano za suyi dace, da za suce da sun sani tuntuni ma, da Abba shine Gwamnan da tuni ma kowa yasha kuruminsa.

Shugaban qungiyar “AKY Brotherhood campaign forum 2023.”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *