Daga Ibrahim Muhammad Kano

Yan Kasuwar Katsina, Daura da Funtuwa mazauna Kano sun yi alkawarin dafawa dan takarar Gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Dan Marke don kaiwa ga nasara a zabe mai zuwa na 2023.

Sun tabbatar da wannan be  a yayin taron da suka shirya a Kano domin nuna goyon baya ga takarar ta Lado tare da mika masa gudummuwar fastoci. Da yake jawabi a taron Sanata Yakub Lado dan takarar Gwamnan ya nuna farin cikinsa ga yan katsina mazauna Kano bisa damuwa da suke nunawa akan irin abubuwa marasa dadi dake faruwa a jihar na rashin tsaro da kuma yanayi na yau da kullum wanda ya shafi kasarnan gaba daya illa dai ya yi muni a jihar Katsina.

Ya ce a yanayi da ake ciki duk Wanda ya tashi ya taimakawa tafiyar PDP tayi nasara kamar ya yi jihadi ne, domin yanda ake kashe rayukan bayin Allah  da basu ci ba basu sha ba,ba laifin fari balle na baki,a kwace dukiyoyinsu aci mutuncin iyalansu , wannan ace ka bada gudummuwa ga wata tafiya da zata kawo karshen wannan abu to suna sa ran in ya mutu a wannan lokaci ya yi shahada.

Lado ya karfafesu da cewa su jajirce su bada gudummuwa a tabbatarda cewa an kauda wannan azzalumar Gwamnati musamman a jihar Katsina da shugabanninta masu mulki suka fito suka fada musu ba zasu iya ba, sai dai kowa yaje ya yi yanda zai iya da kanshi.Wanda abu na farko mai muhimmanci ga shugaba shine ya kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu amma wannan sunce ba zasu iya ba, wannan ya nuna babu Gwamnati kenan.

Ya ce kazo kace kuma zaka bada gudummuwa wannan Gwamnati da ta gaza ta dawo to mutum bai san abinda yake ba,domin ko dabba  na gudun Inda ake cutar da ita,bare dan’adam da Allah yasa masa hankali da tunani.

Sanata Lado Dan Marke  ya ce bashi.da aka ciwo wa jihar Katsina na daruruwan biliyoyi ba Wanda yasan adadinsu sai Allah ya kai su sun bayyanawa Duniya sannan jama’a zasu sani.Dan haka Wanda zai zo ya amshi shugabanci na jihar ba karamin sadaukar dakai bane,domin an yiwa jihar raga-raga.

Ya kara da cewa lokacinda wannan  Gwamnatin ta Katsina ta amshi Gwamnati bata amsheta da bashin komai ba,sai dinbin biliyoyin kudi ma da aka bar musu Saboda haka in Allah ya ka PDP. ga nasara  Allah zai kawo musu hanyoyinda da zasu  iya rike jihar ta yanda za’a iya fitarda Katsina  daga mummunan yanayi na tsaro da hanyoyinda hankalin al’umma zai dawo jikinsu.

Sanata Yakub Lado Dan Marke ya ce yana bada tabbacin maganar tsaro a jihar Katsina shine abinda zai baiwa muhimmanci da izinin Allah in ya kaisu ga nasara da tabbacin in Allah ya yarda Allah zai taimakesu cikin kankanin lokaci maganar tsaron nan zata zama tarihi.

Lado ya yi godiya ga Katsinawa da suka shirya taron bisa karamci da soyayya da suka nuna masa da basu tabbacin a matsayinsu na yan kasuwa in ya kafa Gwamnati zasu bullo da hanyoyinda zasu dada habaka.

Tun farko a jawabinsa Alhaji Aminu Musa shugaban al’uummar  Katsina da Daura mazauna jihar Kano.Kuma shugaban matasa na kasa  na ‘Atiku Project’wanda akafi sani da Aminu Shekarau ya ce makasudin taron shine  sun yarda Lado mutumne jajirtacce mai amana da idan ya ce zai yi zai yi in ya ce ba zai yi ba,ba zai yi ba ,domin ba dan mai amana bane da yanzu baya PDP dan da jam’iyyar batada uwa bata da uba a jihar Katsina a wasu lokuta a baya, amma waiwayowa da ya yi na rike jam’iyyar da kula da jama’a da yake yi suna al’fahari dashi bisa wannan kishi nasa suke mara masa baya.

Ya ce al’ummar Katsina mazauna Kano sune suka dauki nauyin taron dan nemawa jiharsu makoma kuma dan goyon bayan yan takarkari na PDP tun daga na Gwamna har sauran yan takarkari.

Aminu Shekarau ya kokawa dan takarar Gwamnan jihar Katsina Sanata Lado Dannarke kan  kalubalenda ya ce suna dashi a jihar Kano da cewa kowa yasan akwai mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan wasu kabilu amma ba’a ta ba yin mai bada shawara akan matsalolin yan katsina mazauna Kano ba,haka a jihar  Katsina ba’a taba yiba dan haka suna rokon Dan takarar in Allah ya bashi dama su san ana Gwamnati dasu,asan yanda za’a nemi makomar al’ummarsu  a matsayinsu na yan kasuwa asan yanda za’a rika taimaka musu duba da yanda suke samun matsaloli na nuna musu bambamci a kasuwsnci a jihar Kano Mutum na zaune a shago ko kasuwa yana haya amma in an tashi saida shagon, maimakon ayi masa magana sai ace ba dan jihar Kano bane ,sai a nemo dan kano ya saya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *