Daga Ibrahim Muhammad Kano

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kama tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Idris Wada Saleh da wasu mutane guda biyar kan zargin almundahanar Naira biliyan days.

An kama kwamishinan ne wanda kuma shi ne tsohon Manajan Darakta na Hukumar Kula da gyaran Tituna na Kano KARMA,tare da Babban Sakatare na Hukumar sayo kayiyyakin gwamnati, Mustapha Madaki Huguma, da Daraktan Kudi da Bincike da tsare-tsare tare da wasu a yammacin ranar Litinin kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan daya da aka sanya a kasafin gyaran wasu tituna guda 30 da magudanar ruwa a cikin birnin Kano.

Hukumar karɓar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kama tare da tsare kwamishinan ayyuka na tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, Engr Idris Wada Saleh da wasu mutane biyar bisa zargin almundahanar Naira biliyan 1.ajiyar Kadaura24, Solabase ta rawaito cewa an kama kwamishinan wanda kuma shi ne Manajan Darakta na Hukumar Kula da Titin Kano wato KARMA, da Babban Sakatare na Hukumar sayo kayiyyakin gwamnati, Mustapha Madaki Huguma, da Daraktan Kudi, sai kuma Daraktan Bincike da Tsare-tsare tare da wasu a ranar Litinin da yamma bisa zargin karkatar da sama da Naira biliyan 1 da aka yi wa kasafin gyaran wasu tituna guda 30 da magudanar ruwa a cikin birnin Kano Wata majiya tace an biya kudaden da aka core a cikin asusun wasu kamfanoni guda uku.

An bayyana cewa har hukumar saye da adana kayan gwamnati ta bayar da satifiket na rashin amincewa da kwangilar bayan an biya kudin kwanaki goma kafin ba da kwangilar, wanda hakan ya sabawa dokar sayan kaya ta jihar Kano ta 2021,Cesar wata majiya.

“sannan anyi anfani da Kamfanonin na bogi da suke da takardar rubutun wasika guda daya kuma ba tare da sanin in da ma ofishin su ba yake ba.”

‘’Hukumar bin ka’idoji gwamnati ta ce ba a bayar da takardar shedar rashin amincewar ba, saboda hukumar kula da titinan Kano (KARMA) ta ce za a yi aikin gyaran hanyoyin ne ta hanyar aiki kai tsaye, amma takardun da aka basu suka karanta ba su nuna haka ba.

Wadanda aka kama na fuskantar tambayoyi za a kuma gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike da aka akansu.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *