Daga Ibrahim Muhammad Kan

Kungiyar Cigaban unguwannin Indabawa da Kurmawa (INDA -KURMA)ta gudanarda taron cikarta shekaru 20 da kafuwa  a harabar makarantar furamare na Dan’agund

A yayin taron an raba racen kudin jari ga iyayen marayu Mata  tareda karrama wasu muhimmam masu tallafawa kungiya

Da yake jawabi mukaddashin shugaban kungiyar na INDA-KURMA Alhaji Aminu M.Faruk ya bayyana cewa  an kafa kungiyar ne shekaru 20 da suka gabata domin taimakawa cigaban al’ummomin unguwannin Indabawa Kurmawa Unguwar gini da kewaye

Daga nasarorin da kungiyar ta samu ya ce akwai samarda ayyukanyi ga matasa  a ma’aikatu  da horas dasu akan sana’oi,tareda yin haxin gwiwa da Hukumar NDE wajen horasta matasa sana’oi.Da basu tallafi karkashin shirin  NAPEP da UNDP da basu rance  a karkashin kananan Bankunan al’umma

Yace a bangaren ilimi ana horasda yara darasi na ilimi da daukar nauyin biyan malamai da samawa dalibai guraben karatu a manyan makarantu  da sayawa yara katin jarabawa na JAMB,NEC

Haka a harkar lafiya ana kulada tsaftar muhalli da feshin maganin sauro da gudanarda aikin masu larurar ido da riga-kafin sankarau da sauran abubuwa da dama da suka hada da sada zumunci  da shirts  shan ruwa a watan Azumi.

Alhaji  Aminu M.Faruk.yace INDA-KURMA  ta jawo kamfanonin wayoyi sunyi rijista ga yan yankin haka ma ta kira hukumar katin Dan kasa sunyi  sannan suka gudanarda ayyukan samarda ruwansh

Mukaddashin shugaban na Inda-Kurna yace daga matsalolinda take addabarsu akwai rashin samun kudaden shiga da hakan ya jawo musu tsaiko,wajen gina filin sakatariyar kungiyar data mallaka

Kwamishin yansandan jihar Bauci Alhaji Aminu Alhasan Indabawa na daya daga cikin yan yankin da aka karrama bisa gudummuwa da take badawa ga cigaban kungiyar

Da yake jawabi a madadin wadanda aka karrama kwamishinnan yansandan Aminu yace wannan karramawar karfafa musu gwiwane wajen cigaba da bada gudummuwa ga cigaban Kungiyar

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *