Daga Nasiru Adamu
Shugaban karamar hukumar Sabon Gari Hon Muhammad Ibrahim Usman ya kaddamar da alluran shan inna a gundumar Bomo
A lokacin wannan taron shugaban qaramar hukumar ya muna matukar farin cikin sa ganin yadda al’umar gundumar suka fito qwansu da qwarqwatan su domin nuna goyon bayansu ga Jami’an kiwon lafiya don karban wannan alluran.
Shugaban ya ce Nijeriya tana daya daga cikin kasashen nahiyar Afrika wadda kungiyar samar da lafiya ta duniya WHO ta yaba wajen kawar da cutar shan inna a wannan nahiyar
Hakanan shugaban ya baiyyana cewar karamar hukumar Sabon gari ta samar da magunguna na milyoyin Kudi ga asibitocin dake wannan qaramar Hukuma, kyauta domin amfanuwar al’ummar cikinta, kuma tuni al’umma sun fara amfana da su.
Itama a nata jawbin da ta gabatar a gun taron babbar magatakardan má’aikatar lafiya karamar hukumar Sabon Gari Dakta Tariza markus ta bukaci iyaye maza da su ringa baiwa matayensu goyon baya wajen lura da lafiya yayan su domin kaucewa cututtukan dake addabar kananan tara.
Daga karshe ta yaba wa shugaban karamar hukumar Sabon Gari Hon Muhammad Ibrahim Usman abisa kokarin da yake yi na samar da ingantaccen kiwon lafiya a cikin birane da kauyukan wannan karamar hukumar ta Sabon Gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *