Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana babban abinda ya kawo nasarar jam’iyyar NNPP a jihar Kano shine sakamakon irin ayyukan alkhairi da Kwankwaso ya gabatar a lokacin mulkinsa da baya wanda wannan alherinne yake bibiyarsa.
Wannan tasa har yanzu duk abinda ya dauko a jihar Kano al’ummar Kano ke karba wannan ya kawo nasara.

Tsohon sakataren kudi na jam’iyyar PDP na jihar Kano.Hon.Dahiru Arrow Dakata ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai.

Duk dan jihar Kano mai kishi dole ya yiwa Gwamnatin Abba kyakyawan zato sakamakon kowa ya sanshi mutum ne tsayayye,natsastse ,jajirtaccen ma’aikaci mai so da tausayin al’ummar Kano.

Ya tabbatarwa al’ummar jihar Kano da izinin Allah zasu amfana da Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf da al’ummar kasa ma gaba daya domin in akace maganar Kano ta kasa ce gaba daya.

Ya ce al’ummar jihar Kano zasu amfani wannan Gwamnatin ta kwankwasiyya domin kowa ya san Gwamnati ce da ke duba kasa ta ke kallon talaka ta ke so,ta raya shi, a daukaka shi.

Hon.Dahiru Arrow Dakata ya yi nuni da cewa al’ummar jihar Kano sun baiwa wannan Gwamnati mai shigowa hadin-kai ta zabar Abba zasu kuma bashi hadin-kai za su kuma taya shi da addu’oi akan mulki da za’a fara a gama lafiya kowa ya amfana a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *