Daga Ibrahim Muhammad Kano

An shawarci gwamnan jihar kano mai jiran gado.Injiniya Abba Kabir Yusuf akan ya dauki matakai tun daga tushe da zai hada da iyaye masu unguwanni dattawwa da matasa dan ganin an kauda harkar daba a unguwanni, musamman na kananan hukumomin kwaryar birnin Kano.

Wannan shawara Alhaji Abdullahi Baba ne ya bayar da yake zantawa da manema labarai ciki harda jaridar Idon mikiya.

Ya ce duk matsalolin rashin tarbiyya da ake samu a tsakanin yara da ke kaisu ga aikata mugayen laifuka da daba da shaye-shaye na daga irin sakaci da biris da akayi da tarbiyya musamman a matakin unguwanni.

Alhaji Yusuf ya yi nuni da cewa yanzu a halinda ake sai kaga iyaye da al’ummar unguwanni suna ganin ya’yansu suna  halayya na ba daidai ba, amma sai su zura ido ko su boye laifinsu.

Dan haka idan da gwamnati zata kafa kakkarfar kwamiti na tsaro da ladabtarwa da zai kunshi iyaye da dattawa da matasa da wakilan jam’an tsaro da zasu rika sa ido akan tarbiyyar matasa duk wanda ya yi abinda bai kamata ba abi takan iyaye da dattawan unguwanni da jami’an tsaro ba tare da nuna sani ko sabo ba, ayi masa hukunci da doka ta tanada,hakan  zai kawo sauki.

Ya kara da cewa akwai yara da dama sun fi karfin iyayensu,da bai kamata kuma ace sun fi karfin al’ummar unguwanni ba.Sannan a rika daukar matakai akan iyaye da ake samu suna boye laifin ya’yansu a lokacinda suka cutarda al’umma, ta mi kasu ga  hukuma, hakan zai kyautata zamantakewa da ake.

Abdullahi Baba ya ce abin takaici shine yanda mutanen Kano  sukayi biris da rashin kulawa da tarbiyyar ya’yansu su kuma al’umma sun zura ido.Dole sai an hada hannu Gwamnati da sauran al’umma sun shigo za’a sami gyara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *