Daga Ibrahim Muhammed Kano

Zaben Gwamna a jihar Kano.An sami rahotanni hauhawar cin zarafin jama’a ta bangarori daban-daban.In aka kwatanta da zaben shugaban kasa da ya gabata.
Shugaban hukumar Kare hakkin dan’adam ta a kasa reshen jihar Kano.Shehu Abdullahi ne ya bayyana hakan.

Yac ce akwai matsaloli da yawa na take hakkin dan adam da akayi da suka hada da hana mutane yin zaben da rikice-rikice da fasa akwatuna da haifarda tashin hankali a mazabu a rumfunar zabe,wadanda suka fito domin yin zabe basu yi ba.

Ya yi nuni da cewa duk wannan nau’ine na tauye hakkinsu dan sun dade suna jiran lokacin zabe su zo su gudanar da zaben su amma kuma hakan bai yiwu ba.
Shehu Abdullahi ya ce bayan nan akwai matsaloli da suka shafi cin zarafi na dan’adam ta hanyar duka ko wani yanayi da za’a ta ba lafiyarsa da kuma matsaloli na bada cin hanci dan sauransu domin asa mutane mutane su zabi abinda ba ra’ayinsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *