Daga Ibrahim Muhammad Kano

jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta kai koke gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamna, inda ta dage cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna bai cancanci tsayawa takarar ba.

Lauyoyin jam’iyyar APC a cikin karar da suka shigar gaban kotun da ke zamanta a kan titin Miller, sun ci gaba da cewa dan takarar gwamnan NNPP ba dan jam’iyyar ba ne, saboda bacewar sunan sa a cikin rajistar jam’iyyar da aka mika wa INEC. .

Kamar yadda mai shigar da kara ya bayyana a cikin karar da APC ta shigar mai lamba biyar, sunan zababben gwamnan, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, “ba ya cikin jerin rijistar NNPP da ke hannun INEC.”

APC ta ci gaba da cewa, ta hanyar koken cewa, “Kafin zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023, dan takarar jam’iyyar NNPP ya gaza cika sharuddan zama mamba a jam’iyyar, don haka bai cancanci tsayawa takara a zaben gwamna ba bisa tsarin jam’iyyar.

APC ta kuma bukaci kotun da ta soke zaben Abba Kabir Yusuf bisa hujjar cewa APC ce ta samu rinjayen kuri’u na halal a lokacin zaben gwamna.

Mai shigar da karar ya kuma bukaci kotun da ta amince da adadin kuri’un da aka kada a matsayin wanda ba shi da tushe balle makama , don haka a yi la’akari da yadda aka cire adadin kuri’un da aka yi ba bisa ka’ida ba , sannan a dogara da tazarar da za a bari a bayyana zaben gwamnan Kano a matsayin wanda bai kammala ba.

Wadanda ake kara NNPP, dan takararta na gwamna da kuma INEC suna da kwanaki 21 don amsa batutuwan da mai shigar da kara ya gabatar.

A halin da ake ciki dai kotun ta baiwa jam’iyyar APC takardar bukatar duba kayan zaben gwamna, a wani bangare na ci gaba da shari’ar su da NNPP a gaban kotu.

Mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar APC reshen Kano, Abdul Adamu Fagge ya tabbatar da cewa tawagar jam’iyyar APC ta fara aikin duba kayayyakin zaben a daukacin kananan hukumomi 44 na jihar.

Ya ce binciken yana gudana cikin kwanciyar hankali tare da goyon bayan dukkan bangarorin da abin ya shafa.”kuma sunada kwarin gwiwar cewa babu wani cikas da zai hana aikin.

A cewarsa, an baiwa tawagar lauyoyin APC damar samun dukkan kayan aiki kawo yanzu, “jam’iyyar za ta bibiyi lamarin har zuwa ga doka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *