Daga Bello Hamza

Babban Sakataren hukumar kula da iyakokin ruwa na duniya, Mr Kitack Lim ya kaddamar da sabon ginin shedikwatar NIMASA na zamani dake yankin Victoria Island a jihar Legas.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da sabon ginin, Mr Kitack Lim ya bayyana gamsuwar shi bisa jagorancin Ministan harkokin sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo da sauran shugabannin hukumomin dake karkashin ma’aikatar shi.

Ya kuma jinjina kokarin da aka yi wajen samar da sabon ginin, sannan ya jaddada muhimmancin inganta kwarewar ma’aikata don cimma manufar da aka sanya a gaba.

Shima a nashi jawabin, Ministan harkokin sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo ya gode wa babban sakataren dangane da ziyarar da ya kawo Nijeriya don ganewa idanun shi irin cigaban da aka samu a bangaren iyakokin ruwan kasar nan.

Ya kuma bada tabbacin cewa Nijeriya za ta cigaba da aiwatar da manufofin bangaren ta na iyakokin ruwa daidai da na zamani ta hanyar yin amfani da kimiyyar da fasaha.

A nata tsokacin, Shugabar kwamitin majalisar wakilai akan iyakokin ruwa, Misis Lynda Ikpeazu ta yaba da salon jagorancin Shugaban hukumar NIMASA, Dr Bashir Jamoh sannan ta bukaci da ya kara bada himma wajen ciyar da hukumar gaba.

Shugaban hukumar ta NIMASA, Dr Bashir Yusuf Jamoh ya bayyana farin cikin shi ne bisa ziyarar Mr Lim inda ya sanar da shi cewa hukumar ta dukufa wajen ganin ta samar da kyakkyawar yanayi a bangaren kula da iyakokin ruwan kasar nan tare da goyon bayan masu ruwa da tsaki a bangaren.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *