Daga Ibrahim Muhammad Kano
An kafa bankin “MEDEF Non interest Micro Finance” ne a shekara ta 2022 cikin watan Takwas da manufar gudanarda harkar kasuwanci na yau da kullum kuma banbabcinta da sauran bankuna shine tana gudana ne ba tareda ruwa ko riba a ciki ba.
Manajan Daraktan Banking .Ishaq Aliyu Waziri ya bayyana hakan da yake zantawa da yanjarida a jihar Kano.Ya kara da cewa
Bankin na gudanarda harkar kasuwanci daya shafi ajiye kudi da cirewa da tura kudi duk inda akeso da tallawa masu kananan kasuwanci ta basu jari da habaka kasuwancinsu da baiwa manoma rance.
Yace kamar yanda aka sani a halinda ake ciki a kasarnan na matsin tattalin arziki.Sai wadanda suka kirkiri Bankin hadu suka kafa Bankin bisa lurada akwai bukatar irin wadannan bankuna domin “Micro Fanance Bank” Sune sukafi kusa da al’umma.
Ya kara da cewa Bankin nasu na MEDEF sun kafashine bisa lura da halinda ake ciki na tattalin arziki, lalacewarsa da kuma kokarin habakashi yasa masu ruwa da tsaki na Bankin suka zauna suka assasata, kuma da yardar wannan Bankin anyi mata gunshiki mai nagarta an dorata akan hadafi da manufa mai kyau.
Yace izuwa yanzu sun baiwa masu noman Rani samada 100 a Misau da sauran sassa da suke garin Wanda akalla sun bada bashin kudi samada N18,000,000 ga manoma, kuma yanzu haka akwai Karin wasu mutane da suke bukatar tallafin samada Mutum 300.
Ishaq yace Bankin akan kafafunta ta tsaya, dan ganin yanda zata shiga al’amuran cigaban mutane daga kan yan kasuwa zuwa manoma.
Ya yi nuni da cewa akwai matakai da Bankin ke bi kafin bada rance na sanin wa zasu baiwa ?Ta bin diddigi da ka’ida da inganta da harkokinda Wanda za’a baiwa bashin, sai anje an duba gonarsa an ganta anji tarhin gonar, gonace da aka saba yinta ake samun alkhairi a ciki?
Sai da aka bi wadannan ka’idoji aka bada wannan bashin.Kuma sunada tabbacin cewa manoman noma suke da gaske,kuma da yardar Allah zasu sami alkhairi su kuma dawowa da banki kudinta akan lokaci.
Ishaq Aliyu Waziri Manajan Daraktan Bankin na MEDEF yace Bankin duk da an kafa tane a garin Misau, amma babu daga Inda ba’a zuwa daga sassan Bauchi har ma daga wajenta dan a amfana da ita, kuma yanzu ma sun shigo jihar Kano kuma mutane da dama sun bude asusu a bankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *