Daga Ibrahim Muhammad Kano

Hukumar yi wa kamfanoni rijista ta qasa ta yi taro na wayar da kan jami’an tsaro, hukumomi masu yaki da cin hanci da rashawa da sauran kungiyoyi masu zaman kansu.

Taron wanda aka gudanar a jihar Kano ya sami halartar shugaban hukumar ta kasa Garba Abubakar da sauran masu masu ruwa da tsaki na hukumar da yan kasuwa, wakiilan jami’an tsaro da kungiyoyi.

Da yake zantawa da manema labarai shugaban hukumar ta. CAC na kasa Garba Abubakar ya ce taron na wayar da kan jami’ai ne da kumgiyoyi da masu hannu jari da masu gudanar da kamfanoni .
Ya yaba da yanda mutane suka basu goyon baya suka halarci taron.

Garba ya ce anyi bayanai mahalarta taron suma sunyi an kuma yi tambayoyi na abinda ake so a sani an amsa musu.

Yace jami’an tsaro da suke binciken masu laifi na da kyakkyawar rawa da zasu taka wajen gano wanda ya yi al’mundahana ko ya yi amfani da kudi wajen baiwa yan ta’adda ko wanda ya kwashi kudi ya boye taron zai saukaka aikin jami’ai za suyi amfani da rijista da suka kawo daga ko’ina ba sai lallai sun nemi bayanai daga hukumar ba, hakan zai taimaka musu wajen aiki.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *