Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana cewa ranar damakwaradiyya ba kawai na tattauna wasu matsaloli ne kurum ba,rana ce ta mai yan Nijeriya zasu iya yi su bada gudummuwa dan kasar ta samu ta kai ga gaci.

Shugaban cibiyar nazarin Damakwaradiyya na gidan malam Aminu kano dake karkashin jami’ar Bayero dake gidan Mumbayya.Farfesa Habu Muhammad ne ya bayyana hakan da yake zantawa da yan jarida a yayin taron ranar Damakwaradiyya da cibiyar ta shirya da hadin gwiwar wasu kungoyi.

Ya ce yau shekara zama da 20 da samuwar Damakwaradiyya a kasar nan talauci da da katutu yake,yunwa ta yi yawa rashin lafiya babu magani a asibiti yan ta’adda sun addabi kasa,harkar tsaro ta zama halin ha’ula’i yana dakyau dukkanmu a shigo ayi hobbasa aga an sami canje-canje wanda zai maganin wahalhalu da aka sha a baya.
Shima Furofesa Kamilu Fagge Wanda shine ya wakilci Mataimakin shugaban jami’ar Bayero Farfesa Sagir ya ce a wannan Damakwaradiyya an sami cigaban daban-daban wannan kima ba shine karon farko da aka fara kokarin tsarin Damakwaradiyya ba a kasar na.A lissafi.wannan shine na uku.
Ya ce babban cigaban da aka sami shine an sami tsawon shekaru Samada 20 da tsarin ya dore sauran tsarukanda akayi guda uku in aka hada su ko rabin wannan basu kai ba, wannan cigaba ne.Sannan an sami cigaba na Samar da kayayyakin more rayuwa daga kananan hukumomi zuwa jihohi zuwa gwamnatin tarayya.
Farfesa Kamilu fagge ya ce cikin shekaru an sami nasara abubuwa da suke tasowa kamar kasar zata rushed,amma sai a zauna a tattauna a sami mafita.
Sai dai kuma a wani bangaren akwai abubuwa da za’a ce,har yanzu akwai rina a kaba na farko duk lokacinda za’ayi tsarin Damakwaradiyya a Nijeriya yan kasa na shaukin wannan tsarin saboda ana ganin tsari ne na kawo zaman lafiya da cigaba da zai sa shugabanni su rika yin abinda mutane sukeso.
To amma a.tsawon shekaru wadannan abubuwa sun kusan gagaran kundila na farko tsarin zaman lafiya duk da an iya warware matsaloli amma kuma an sami tashe-tashen hankula a wurare daban-daban wanda a tarihin Nijeriya ba’a taba samun tashin hankali da yawa a lokaci daya ba kamar a wannan tsari ba.
Sannan kuma an sami ci baya Dan maimakon halin rayuwar jama’a ya inganta domin gwamnati tasu ce,su zasu zabi shugabanni sai gashi cikin shekaru 25 din nan halin rayuwar jama’a ta yi kasa domin talauci da yunwa da fatara ya kai kashi 75 na yan kasa na fama da talauci.

Wanda kuma abinda yasa mutane ke shaukin Damakwaradiyya shine zata bada dama a fita daga wannan sannan akwai matsalar cin hanci da rashawa da ta yi katutu ya zama yanzu duk inda ka daga a kasashen Duniya mun zama abin kallo da yiwa dariya domin cin hanci da rashawa ana yin sane da gadara maimakon ace wasu wurare da ake ana sakaya shi amma nan da gadara ake mutane su fito tun ana maganar maganar kudi na dubbai aka zo ana miliyoyi yanzu ana biliyoyi yanzu in ka bincika wasu tiriliyoyin kudi suka ci kuma su zauna mursisi ba abinda za’ayi musu.

Farfase Kamilu Fagge ya ce batun ci baya da aka samu shine na yanda hauhawar farashi take kullum, yanzu har dan Najeriya ya zamanto baya mamakin ya sayi yanzu in anjima ya koma kasuwa ya ji kudinsa ya karu wadannan sune ake ganin ci baya dan haka ake irin wannan taro na Damakwaradiyya azo a tattauna wadannan matsaloli a samo hanyar da za’a fita.

Taron dai ya sami halartar yan siyasa da masana da dama ciki har da tsohon Gwamnan jihar Kano.Sanata Malam Ibrahim Shekarau da Dokta Bugaje da Malam Ibrahim Khalil da sauran mutane da sukayi jawabai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *