Daga: Umar Faruk Brinin Kebbi

Dan takarar jam’iyyar APC wanda ke neman a zabe shi don wakiltar mazabun Kebbi ta arewa, Dakta Hussaini Suleiman Kangiwa ya yi Allah wadai tare da karyata wata waka mai suna “Kadangaren bakin tulu” da aka danganta a matsayin daya daga cikin wakar yakin neman zabensa.

Dakta Hussaini Suleiman Kangiwa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin kebbi.

A cewarsa, wakar ta kunshi wasu kalamai na nuna kyama da kalamai masu alaka da adawar siyasa wadanda a cewarsa za su iya haifar da rashin hadin kai a tsakanin al’ummar jihar.

Ya kuma yi kira ga wanda ke da alhakin wakar da ya janye ta ya bayar da hakuri na musamman ko kuma ya fuskanci shari’a kan abin da ya aikata. Wanda jama’a na ganin cewa kamar Dakta Hussaini Suleiman Kangiwa ne ya dauki nauyin rera wakar, inji shi.

Dan takarar Sanata mai neman wakiltar mazabun Kebbi ta Arewa ya ce ya shiga siyasa ne domin samar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban al’ummar jihar ta Kebbi inda ya ce lamarin siyasi ba a mutu ko ayi rai ba ne, acewarsa.

Haka zalika ya yi kira ga sauran jama’a ko kuma wadanda suka saurari wakar ko suke da ita da su yi watsi da ita domin ba shi da ilimi kuma ba a yi shi da yardarsa ba, inji Dan takarar kujerar Sanata na kebbi ta arewa Dakta Hussaini Suleiman Kangiwa.

Wasu daga cikin magoya bayansa, Aliyu Ibrahim Gamuzza da Akilu Haruna Yeldu sun bayyana Dakta Hussaini Kangiwa a matsayin dan siyasa mai son zaman lafiya kuma jigo a aikin al’umma, inda suka bukaci sauran magoya bayansa da sauran jama’a su gudanar da siyasa kamar yadda hukumar zabe ta kasa INEC da kuma kundin tsarin mulkin tarayya ya tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *