Daga Muhammad Shamsudeen Yobe
Dan takarar Gwamnan jihar Yobe a karkashin jam’iyyar PDP, a zaben 2023 mai zuwa, Hon. Shariff Abdullahi ya karyata jita-jitar janye takarar sa tare da mayar da martanin cewa wannan farfaganda ce maras tushe da makama. Ya jadada cewa babu wannan magana; ba a yi ta ba kuma babu alamarta, face kawai karya ce tsagwaronta wadda wasu maras tunani suka kirkira tare da yada ta domin sanyaya gwiwar magoya bayansa.
Hon. Shariff Abdullahi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labaru mai dauke da sa hannunsa, wadda aka raba wa yan jaridu ranar Litinin a Damaturu, babban birnin jihar Yobe. Yayin da sanarwar ta kara da cewa, abin da masu iri-iren wannan gutsiri-tsoma basu sani ba shi ne, PDP jam’iyyar ce mai tsari kuma mai hadin kai tare da bin dokokin sau da kafa- wannan yunkurin bai gaza shure-shure baya hana mutuwa ba.
“A hannu guda kuma, idan abin a tambayi masu yada wannan karyar ne; shin idan takara zai janye takarar sa a daidai wannan lokacin, shin akwai damar sake wani zaben fidda-gwani, ko a haka wanda aka janye wa zai shiga babban zabe? Sannan anya masu yada wannan farfagandar sun karanta dokokin zabe na 2022, tsare-tsare da tanade-tanaden da suka kafa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC)”?
“Saboda haka, babu inda na bayyana hakan a rubuce, kuma ban yi zancen da kowa ba kan cewa zan janye ba, ba a yi wannan ba kuma halin da ake ciki babu wannan batu. Kuma idan PDP za ta sauya dan takaran da ya ci zaben fidda-gwani sai ta dauko wani can daban wanda, dan APC ta bashi takarar, alhalin tana da wadanda suka shiga zaben fidda-gwanin dani; ai idan ma hakan ne dayansu ya cancanta. Kuma kuna ga zai yuwu dan siyasa Irina zai janye takarar ba tare da tuntubar al’ummar ta ba”?
Hon. Shariff ya bayyana ya yi kira ga al’ummar jihar Yobe, musamman yan jam’iyyar PDP su yi watsi da wannan karya maras tushe. Tare da jaddada cewa zai ci gaba da rike amanar da suka damka masa ta takarar Gwamnan jihar Yobe a zabe mai zuwa a 2023 in sha Allah. Kuma ya ce cikin yardar Allah jam’iyyar PDP ita ce da nasara saboda su suke da cikakken goyon bayan Jama’a.
“Sannan kuma ina kara kira ga al’ummar jihar Yobe baki daya, musamman yan jam’iyyar PDP mu ci gaba da juriya da cikakken hadin kai, saboda sai ta haka zamu samu nasara. Kuma ya na daga cikin burinmu samun cikakken hadin kan baki dayan al’ummar jihar Yobe, zamu yi aiki da kowa wajen ganin mun sake farfado da jiharmu wajen magance kalubalen da mu ke fuskanta, wanda sanin kowa ne cewa al’ummar jihar Yobe suna da bukatar canjin gwamnati, saboda yadda APC ta dagula al’amurra tare da mayar da hannun agogo baya.”
“Ci gaban jihar Yobe zai yuwu ne ta hanyar hada hannu da karfi, mutunta juna, wanda ko shakka babu muna da manyan kalubalen da ya dace mu fuskanta wanda bisa ga hakan ne muke ci gaba da aiwatar da ingantattun tsare-tsare da shiri mai ma’ana wajen tunkarar su. Muna da kwarewar da zamu sake gina jiharmu; ba zance ne na babatu da fada a baki ba, abu ne a bayyane; zo ka nuna mana abin da ka taba yiwa al’ummar jihar Yobe, amma ba ka shigo ka yi surutu ka gudu ba. Ko a zabeka ka gudu sai bayan wata daya ko biyu ba, ko sai lokacin zabe ka zo.” In ji shi.
Ya ce lokaci yayi wanda al’ummar jihar Yobe za su bambance dan duba da na kabewa, saboda yanzu duniya ta na karni na 21 ne- zamanin ci gaba wanda shugaba zai baje kolin kwarewarsa da ilimi, ba a siffar yan-daba ba. Ya ce bai dace al’ummar Yobe su sauraron yan siyasa masu kama da yan-sara-suka ba, mayun mulki, yan-tayi-dadi, yan siyasar da ba a ganin fuskokin su sai lokacin zabe; bayan sun karbi kwangila su zo domin yiwa jama’a burga. Daga nan ba a kara jin muryar su sai bayan shekaru hudu (4).
“In sha Allah muna kara tabbatar wa da al’ummar jihar Yobe cewa muna nan kan bakarmu kuma da yardar Allah za mu cire jaki daga cikin gonar duma- in sha Allah.” Ta bakin Hon. Abdullahi.
A karshe ya bayyana ya mika sakon godiya ga shugabanin jam’iyyar PDP a jihar Yobe da na kasa baki daya, kusoshin jam’iyyar, yan takara a kowane mataki a nan jihar Yobe da kasa baki daya, dattawan PDP, matasa maza da mata da daukwacin yayan jam’iyyar PDP da al’ummar jihar baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *