Deaga Bello Hamza, Abuja

Dan takarar kujerar gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal ya yi alkawarin bunkasa harkokin noma a sassan jihar da zaran ya samu nasarar bdarewa kujerar gwamnan jihar a zaben da ke tafe. Dauda Lawal ya bayyana haka ne a tattaunawa da wakilinmu a garin Gusau ranar Talata.

Ya ce, kasancewar kashi 80 na al’umma jihar Zamfara manoma ne da suka shahara a fannin noma  damuna dana rani suna kuma noma a bubuwan da suka hada da Gero, Dawa, Masara Shinkafa, Gyada Auduga da Wake. ‘’A kan haka zan tabbatar da manoma na samun dukkan kayan aiki noma da suka hada da takin zaman, maguguan kashe kwari da sauransu a kan lokaci. bai kamata a ce ana fuskantar mastalar karancin abinci ba a Jihar Zamfara, musamman ganin muna da al’umma masu kwazo da zimmar neman na kansu’ inji shi.

Don tabbatar da samun nasarar matakan bunkasa harkar noma, Alhaji Dauda Lawal ya yi alkawarin kawo karshen ayyukan ta’addanci tare da samar da ayyukan yi da dimbin matasan jihar. A kan haka ya nemi al’umma su fito qwansu da qwarqwatar su wajen kada kuri’ar su ga jami’iyyar PDP a zabe mai zuwa don ta haka ne za a samu tabbacin fitar da al’umma daga halin matsalar rayuwa da gwamnatin APC ta jefa su’’, inj ji shi

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *