Daga Bello Hamza, Abuja

Dakta Dauda Lawal ya zama sabon gwamnan jihar Zamfara bayan ya sha rantsuwar kama aiki a Gusau babban birnin jihar. Ya karbi mulki daga wurin Bello Matawalle.

Dauda Lawal ya zama sabon gwamnan jihar Zamfara bayan ya sha rantsuwar kama aiki a Gusau babban birnin jihar.

 

Ya karbi mulki daga wurin tsohon gwamnan jihar Bello Mohammed Matawalle.

 

An yi bikin ne a filin baje koli da ke Gusau, a birnin jihar Zamfara.

 

Shi ma mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mallam Mani Muni ya sha rantsuwa.

Sabon gwamnan zai soma aiki ne a yayin da jihar ke fama da matsalar tsaro ta ‘yan bindiga wadanda ke kashe mutane tare da sace wadansu domin karbar kudin fansha.

Jaridar Idon Mikiya na masa fatan alhairi.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *