Daga Ibrahim Muhammad Kano

Daya daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasa a jihar Kano, Dr. Saleh Musa Wailare ya bayyana fatansa na cewa sabuwar zababbiyar Gwamnatin jam’iyyar NNPP za ta yi aiki ba tare da son kai ba wajen ci gaban jihar Kano.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai a Kano, inda ya kara da cewa Injiniya Abba Kabir Yusuf zai jagoranci jihar da gogewarsa ta fuskar siyasa da sana’a domin kawo ci gaba a fannin ilimi, tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa.

Dokta Wailare ya sake nanata cewa, “Na yi farin cikin bayyana cewa Mai Girma Injiniya Abba Kabir Yusuf zai bunkasa jihar Kano a kowane fanni bisa la’akari da kwarewarsa.


Dr. Wailare wanda shi ne dan takarar majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar PDP daga mazabar Dambatta/Makoda a zaben da akayi a ranar 25 ga watan Fabrairu, ya ba da tabbacin cewa yanzu dimokuradiyya ta kara samun karbuwa a Najeriya.

Don haka, ya yi kira ga al’ummar jihar da su goyi bayan sabuwar Gwamnatin domin ta kai ga gacin kyautatawa cigaban Kano.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *